NFHS-5: Teɓa na kara yawa a jikin Indiyawa - kuma hakan babbar matsala ce

    • Marubuci, Daga Geeta Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
  • An wallafa

Wani bincike da gwamnatin India ta gudanar ya nuna cewa teba na kara yawa a jikin 'yan kasar, kuma masana harkokin lafiya sun yi gargadin cewa lamarin zai tabarbare idan ba a dauki matakin gaggawa na shawo kansa ba.

A baya dai ana ganin matsalar teba a matsayin abin da ya shafi masu hali a Yammacin Duniya, sai dai a shekarun baya bayan nan tana shafar kasashe masu matsakaici da masu karamin karfi - kuma tana yaduwa sosai a India.

A lokutan baya can India ta yi suna a matsayin kasar da ke fama da tamowa da mutane marasa kiba, amma a shekarun baya bayan ta shiga cikin kasashe biyar da ke fama da masu teba.

Wani kiyasi da aka yi a 2016 ya bayyana cewa 'yan kasar India miliyan 135 ne suke fama da teba. Wannan adadi, a cewar masana harkokin lafiya, yana karuwa sosai cikin sauri kuma yawan masu kiba yana maye gurbin adadin marasa kiba.

Binciken baya bayan nan da hukumar kula da lafiyar iyali ta kasar (NFHS-5) ta yi ya nuna game da lafiyar iyali da walwalarsu cewa kusan kashi 23 na maza da kashi 24 na mata suna da girman jiki da ya haura da fiye da kashi 25 - wato kashi kashi hudu daga kididdigar da aka yi a shekarar 2015-16.

Binciken ya kuma nuna cewa kashi 3.4 na kananan yaran da ke da shekara biyar zuwa kasa suna fama da matsalar teba idan aka kwatanta da kashi 2.1 a shekarar 2015-16.

"Muna cikin babbar matsalar teba a India da ma duniya baki daya, kuma ina tsoron cewa nan ba da jimawa ba lamarin zai zama annoba idan ba a dauki mataki ba," in ji Dr Ravindran Kumeran, wani likitan fida a birnin Chennai (Madras) kuma wanda ya assasa gidauniyar Obesity Foundation of India.

Dr Kumeran yadora alhakin matsalar kan gudanar da rayuwa ba tare da motsa jiki ba da kuma cin abincin da ke sanya kiba shi ya sa "yawancinmu, musamman wadanda ke zaune a biranen India, muke fama da teba".

Wani gwaji da ake Hukumar Lafiya ta Duniya ke gudanarwa da ke karkasa nau'ukan kiba - masu matsakaiciyar kiba da masu fama da teba - ya bayyana cewa duk wanda ya kai nauyin 25 zuwa sama yana matsayin mai fama da teba..

Sai dai Dr Kumeran da sauran masana harkokin lafiya na ganin ya kamata a kasashen Kudancin Asia a rage wannan lamba ta gwaji da maki biyu saboda "muna da kasadar fadawa cikin masu teba", abin da ke nufin nana da nan ake samu masu katon ciki fiye da sauran kasashe.

Hakan na nufin za a rika ayyana duk dan kasar India da ke da nauyin maki 23 a matsayin mai fama da larurar teba.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, yawan kitse a jiki yana haddasa kasadar kamuwa da cutukan da suka hada da kansa nau'i 13, cutar-sukari nau'i na biyu, ciwon-zuciya da na huhu.

Kuma a bara, an gano cewa teba ta kashe kimanin mutanen miloyan biyu da dubu dari takwas a fadin duniya.

Dr Pradeep Chowbey, tsohon shugaban kungiyar International Federation for the Surgery of Obesity and Metabolic Disorders (Ifso), ya ce "duk karin kilogiram 10 a jikin mutum yana rage rayuwar mutum da shekara uku.

Don haka, idan mutum ya kara kiba da kilogiram 50, zai iya mutuwa shekara 15 kafin lokacinsa."