Gane Mini Hanya: Tsarin ilimin ƴaƴan makiyaya a Najeriya
An wallafa
Danna hoton sama domin sauraren hirar
Makiyaya a baya-bayan nan sun zama kurar baya ta fuskar ilimi, sakamakon koma-baya da ilimin makiyaya na Nomadic Education.
Wasu masana dai na alakanta rashin ilimin da daya daga cikin dalilan da ke sa ‘yan ta’adda ke ribatarsu.
Domin dakile hakan ne wasu jihohi a arewacin Najeriya suka fito da wani tsari na ilmantar da ‘ya’yan makiyayan a makarantun gwamnati a lokacin hutu.
Jihar Bauchi ce ta fara bullo da wannan shiri, kuma kwamishinan ilmin jihar, Dr Aliyu Usman Tilde ya shaida wa Usman Minjibir yadda tsarin yake.