Antonio Guterres: Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na ziyarar-aiki a Najeria

Buhari da guterres

Asalin hoton, Buhari da guterres

An wallafa

A ranar Talatar nan 3 ga watan Mayu ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya isa Najeriya domin soma ziyarar kwanaki biyu.

Babban Jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya je Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda ya gana da Gwamna Babagana Umara Zulum, da kuma iyalan mutanen da rikicin Boko Haram ya yi sanadin rasa rayukansu.

Kazalika Sakatare Janar din zai gana da shugabannin addinai da na kungiyoyin mata da matasa da kuma shugabanin kamfanoni masu zaman kansu.

Baya ga wadannan mutane da zai gana da su, zai kuma gana da jami'an difilomasiyya da ma wadanda ke sansanonin ƴan gudun hijra a jihar Borno.

..

Antonio Guterres zai kuma duba irin kalubalen da ake fama da shi a game da bangaren tsaro a Najeriya.

Kafin zuwansa Najeriya, sai da jami'in Majalisar Dinkin Duniyar ya kai makamanciyar wannan ziyarar a wasu kasashen yammacin Afirka.

Daga cikin kasashen akwai Burkina Faso da Senegal da kuma Jamhuriyar Nijar.

A yayin ziyararsa a Jamhuriyar Nijar, Antonio Guterres, ya gana da shugaban kasar Bazoum Muhammed, inda ya yaba da kokarin da dakarun kasar ta Nijar ke yi wajen murkushe 'masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.

A jawabinsa game da kalubalen tsaro a yankin Sahel, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar, ya ce "Ya kamata hukumomin kasa da kasa su san da sanin cewa tashe tashen hankula da kuma ayyukan masu tayar da baya a yankin na Sahel ba magana bace ta yanki ko ta kasashen Afirka bace kawai, batu ne da ya shafi duniya baki daya."

Ya ce "Zan ci gaba da neman kudi wadatattu domin fuskantar wannan kalubale, a yanzu na ga namijin-kokarin da sojojin Nijar ke yi wajen murkushe 'yan ta'adda."

Antonio Guterres ya ce yakamata hukumomin kasa da kasa su zuba kudi wajen bayar da horo da samar da kayan aiki ga dakarun kasar Nijar.