Yarjejeniyar Birtaniya kan masu neman mafaka: Shin Rwanda wurin kwanciyar hankali ne ko kuma fargaba?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Lucy Fleming
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
A sau da dama, masu kai ziyara kasar Rwanda kan yaba da tsarin kasar ganin yadda abubuwa ke tafiya yadda ya kamata.
Tana da tsari da tsafta, ga kuma wuraren masu korayen ciyayi da shuke-shuke - kana hanyoyin sadarwar intanet din na da kyau a Kigali babban birnin kasar.
Kowa na biyan haraji; kana ayyuka na tafiya daidai; hanyoyin akwai tsaro - gwamnati na kiran ta a matsayin kasa mafi tsaro a cikin kasashen duniya".
Mu dauki misalin annobar korona. Kasar Rwanda ba ta kasa a guiwa ba wajen tunkarar shawo kan matsalar yaduwar cutar korona: an aiwatar da dokar hana fita cikin sauri tare da tilasta bin dokar.
Yanzu haka fiye da kashi 60 bisa dari na yawan al'ummar kasar an yi musu allurar rigakafi.
Amma kuma, abubuwan da ke boye karkashin wadannan dokoki da kuma filayen shuke-shuken furanni akwai wata fargaba.
Idan ka shiga wata mashaya kuma ka fara wata muhawara mai cike da ce-ce-kuce, za a iya taka maka birki - kana akwai yiwuwar a kai rahoton halayyar ka wajen hukuma.

Asalin hoton, Getty Images
Ana daukar tsattsauran mataki kan wadanda ake ganin sun zama barazana.
"Tana yanayi da kasar Switzerland din Afirka, amma kasa ce mai cike da abubuwan fargaba da kuma mulkin-danniya," in ji Michela Wrong, marabuciyar wani littafi a kan kasar Rwanda da aka yi wa lakabi da Do Not Disturb, a hirarta da BBC.
A ranar Asabar din karshen ko wane wata, kowa da kowa na haduwa a cikin unguwarsu don tsaftace muhalli - ana share tituna, tare da kwashe shara. Ana kiran wannan Umuganda, wanda a harshen Kinyarwanda ke nufin ''Aikin Gayya''.
Wani dan kasar Rwanda, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa babu wata doka da ke tilasta wa mutane halartar aikin-gayya na Umuganda - amma akwai fargabar za a lakaba maka wani suna, cewa wani zai kai kararka, cewa za a saka sunanka a matsayin mai tayar da zaune-tsaye.
Makarantar koyon tuki da azuzuwan koyon harsuna
Ko wane sansani da aka tura masu neman mafaka a karkashin sabuwar yarjejeniyar Birtaniya ka iya kasancewa masu kyakkyawan tsari ne - ba sansanonin 'yan gudun hijira da a wasu lokuta ka saba gani da tantuna ko rumfunan ke da da aka manna a kan kaya ba.
Kasar, wacce ke da yawan al'umma miliyan 13, ta riga ta karbi bakuncin masu neman mafaka 'yan Afirka fiye da 900 daga kasar Libya tun a shekarar 2019 - a karkashin yarjejeniyar hukumar lura da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU).

Asalin hoton, AFP
An ajiye su a garin Gashora, mai nisan kilomita 60 daga birnin Kigali. Hukumar UNHCR ta bayyana cewa ba sansanin 'yan gudun hijira ba ne, amma wuri ne na wucin-gadi - kuma an riga an sauya wa fiye da rabin su wurare zuwa kasashen Sweden, da Canada, da Norway, da Faransa da kuma Belgium.
Wurin na Majalisar Dinkin Duniya, wanda gini ne na dindindin ne da ke da nufin koya wa wadanda suka shiga mawuyacin hali a sansanonin kasar Libya, sana'o'in da za su taimaka musu shiga sabuwar rayuwa. Sansanonin na da makarantar koyon tukin mota kana tana da azuzuwan koyar da harsuna da dai sauran abubuwa.
Amma lokacin da kasar Denmark ta sanar a bara cewa tana shirin gudanar da irin wannan yarjejeniya da Birtaniya ta kaddamara, kungiyar AU ta nuna soki lamiri.
"Irin wannan yunkuri na dakile kaura daga Afirka zuwa kasashen Turai nuna kiyayya ne kuma ba abin da za a amince da shi ba ne" ta bayyana a cikin wayan Agustan bara.
Afirka na daukar dawainiyar kashi 85 bisa dari na yawan 'yan gudun hijira na duniya ''galibi a cikin mawuyacin hali, a yayin da kashi 15 bisa dari kacal ne kasashen da suka cigaba ke daukar dawainiya'', in ji ta.
Wrong ta kira wannan a matsayin "yarjejeniyar son rai da rashin tunani''.
"Wani darasi na tsoratarwa ne ga masu neman mafaka… duk wanda ya yi kokarin tsere wa musgunawa a Afirka zai jin tsoron a tasa keyarsa zuwa kasar Rwanda," ta bayyana.
Ba kamar ayyukan hukumar UNHCR ba, cikakkun bayanai kan shirin na kasar Birtaniya da aka fitar, sun yi nuni da cewa masu neman mafaka za su zauna a kasar Rwanda na tsawon lokaci - ''don su samu natsuwa da kuma tsayawa da kafafunsu'', kamar yadda sakataren harkokin cikin gida ya bayyana.
Babu wani tabbaci kan ko mutane nawa ne kasar Rwanda za ta amince ta karba, idan aka duba cewa kasa ce mafi cunkoson jama'a a Afirka, amma kuma Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce za ta karbi dubban daruruwa a cikin shekaru masu zuwa''.
A wajen birnin Kigali, Wrong ta bayyana cewa yanki ne na manoma masu karamin karfi, inda ko wane takun fili ake noma a kansa, kuma ba shi da isasshen wuri da zai dauki yawan 'yan gudun hijirar''.
Gurfanar da masu amfani da shafin YouTube
Babu wanda ke tsammanin nuna wata adawa a cikin gida kan matakin - a yayin da masu sukar lamirin Shugaba Paul Kagame, mai shekaru 64, kana wanda ya jagoranci dakarun da suka kawo karshen kisan kare dangin shekarar 1994, kana ya zama shugaban kasa tun daga shekarar 2000, ke yin nadama.
A watan da ya gabata ne, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto game da gurfanar da masu amfani da shafin YouTube akalla takwas a bara, da ake dauka amtasayin masu sukar gwamnati.
An yanke wa daya daga cikin su hukuncin daurin shekaru bakwai, a bisa nadar wani faifen bidiyo tare da sukar yadda sojoji ke tilasata wa mutane fita daga gidajensu lokacin rushe unguwannin marasa galihu.
Masu yi wa kasar Rwanda aiki yayin zaman mafaka a waje sun rika farauta tare da kisan masu sukar da suka tsere daga kasar - ko kuma ta bangaren Paul Rusesabagina, manajan otal din da ya ceci rayukan mutane fiye da 1,000 lokacin kisan kare dangin, kana wanda aka shirya fim din nan na masana'antar shirya fina-finai Amurka Hollywood da ake kira Hotel Rwanda a kan sa aka gurfanar.

Asalin hoton, Reuters
Bayan kisan kare dangin - wanda aka hallaka mutane 800,000 - Rusesabagina ya zama dan asalin kasar Belgium kuma ya yi amfani da shahararsa wajen fitowa ya yi magana kan abin da ya bayyana mulkin Shugaba Kagame na danniya.
Amma a shekarar 2020, iyalansa sun bayyana cewa an sace shi a yayin da yake wucewa ta Dubai aka kai shi kasar Rwanda kana aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 a gidan-yari kan mara wa kungiyar 'yan tawaye baya.
'Yarsa, Carine Kanimba, ta shaida wa BBC cewa Rwanda ba ta mutunta 'yancin bil adama: "Rwanda mai mulkin kama-karya ce, babu 'yancin fadin albarkacin baki, babu dimokuradiyya.
A zaben da ya gabata shugaban kasar ya samu galabar cin zaben da kashi 99 bisa dari, wanda hakan yan una cewa wannan ba dimokuradiyya ba ce.
"Na kasa gane dalilan da suka saka gwamnatin Birtaniya za ta yanke shawarar aikewa da mutanen da ke fuskantar barazana zuwa kasar da ta yi kaurin suna wajen gallaza wa mutane.''
Soyayyar Jam'iyar Conservative
Watakila dalilan sun danganci Mista Kagame, mai tsawon kimanin kafa shida, ga kwarjini, kana mutum ne mai goyon bayan kungiyar wasan kwallon kafa ta Arsenal. Shugabannin kasashen Yamma da dama - wadanda ke jin nauyin rashin yin wani abin a zo a gani wajen dakile kisan kare-dangin da a waje ake kallon Rwanda da shi - yake ba su sha'awa.

Asalin hoton, AFP
"Yana da matukar basirar gano batutuwan da ke saka shugabannin kasashen Yamma gaza barci, tare da gabatar musu da hanyoyin warware matsaloli masu inganci da saukin kashe kudi,'' in ji Wrong, tana mai nuni da yadda aka aike da dakarun Rwanda zuwa kasar Mozambique a shekarar da ta gabata don fafatawa da mayaka masu jihadi.
A shekarar da ta gabata, Mista Kagame ya bayyana cewa za bai wa 'yan gudun hijira cibiyoyi "a bisa abubuwan suka danganci jin kai." Daya daga cikin 'yan adawa kadan na Rwanda ya bayyana cewa duka game da batun kudi ne.
Kasashen Yamma sun yaba da cigaban tattalin arzikin kasar Rwanda cikin sauri tun bayan kisan kare dangin, kana da cewa batun cin hanci da rashawa ba wani abin damuwa ba ne - duk da cewa kungiyoyi masu bayar da tallafi sun sanar da gargadi game da 'yancin biladama.
Soyayyar da ke tsakanin Jam'iyar Conservative ta Birtaniya da kasar Rwanda ta fara ne a shekarar 2007, yayin yin adawa da wani abu da ake kira Project Umuabano wanda Andrew Mitchell ya kirkiro.
Tsohon ministan raya kasa ya shirya wa 'yan majalisar dokoki tsarin fita wajen a ko wane watan Agusta don gudanar da ayyukan raya kasa - tare da koyar da wasan kurket.
Kungiyar bayar da agajin wasan kurket da ake dangantawa da aikin ta fara tara kudaden tallafi, kuma shekaru kadan da suka gabata aka bude katafaren filin wasan kurket na zaman da ake kira Gahanga Cricket Stadium, ko kuma Kicukiro Oval, a wajen birnin Kigali.
Wasu na yi wa yarjejeniyar masu neman mafakar kallon tsari mai inganci wajen gyara martabar Rwanda, a yayin da kasar ke shirin karbar bakuncin taron koli na kasashe renon Ingila a cikin watan Yuni.
Amma mai magana da yawun gwamnatin kasar Rwanda ya musanta zargin masu sukar lamirin gwamnatin, yana mai cewa babu wanda aka gallaza wa a Rwanda kan fadin albarkacin baki.
"Mun san irin halin da mutane daga kasashe irin wadannan suka shiga, kana wannan wuri ne da za su kasance cikin tsaro da kwanciyar hankali, za a basu kariya kana za su yi rayuwa cikin mutunci tare da samu damar inganta basirar da suke da ita,'' Yolande Makolo ya shaida wa BBC.











