Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An fara neman wanda zai maye firaministan Pakistan Imran Khan da aka tsige
An bukaci masu neman mukamin firaministan Pakistan da su gabatar da takardardunsu nan da wasu sa'oi kafin cikar wa'adin gabatarwar, bayan da majalisa ta tsige Imran Khan daga mukamin.
A ranar Litinin ne 'yan majalisar dokokin kasar za su yanke shawara a kan wanda zai gaji Imran Khan, wanda aka cire daga mukaminsa na firaminista a kuri'ar yanke kaunar da aka kada bayan abokan hadakar gwamnatinsa sun juya masa baya.
Suna dai zarginsa da tabarbarewar tattalin arzikin kasa da kuma gaza cika alkawuran da ya dauka.
Masu sharhi na ganin cewa jagoran 'yan hamayya Shehbaz Sharif, wanda dan uwan tsohon firaministan kasar Nawaz Sharif ne, shi zai gaji kujerar firaministan.
Mr Khan dai na ganin makarkashiya ce ta kasashen waje da aka yi masa, inda ya dora alhaki a kan musamman Amurka, aboda abin da ya ce manufofinsa na kasashen waje. Ya lashi takoin cewa ba zai amince da shigo musu da wata gwamnati ta kasashen waje ba.
Imran Khan, wanda ada ake wa kallon gwarzon kasar saboda irin taka rawar da ya yi a wasan kurket, ya zamo firaministan a 2018 tare da samun goyon bayan sojin kasar.
To amma masu sharhi sun ce sojojin kasar sun harzuka da shi saboda abin da suka ce gazawarsa wajen cika alkawuran da ya dauka na inganta harkokin gwamnati.
Tare kuma da nuna sako-sako wajen korar wadanda suka samu sabani da sojojin, cikinsu har da shugaban hukumar leken asirin kasar da gwamnan Punjab.
Wakilin BBC ya ce a bara sabanin da aka samu tsakanin bangarorin biyu da kuma 'yan hamayya, ya nuna cewa tun a lokacin suka fara kokarin daukar matakin sauke shi.