Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙin Ukraine: Yadda kalaman kunyatarwa na shugaban Ukraine ke jan hankalin Turawan Yamma
- Marubuci, Paul Adams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent
- An wallafa
Yayin da dakarunsa ke fafatawa ba ƙaƙƙautawa a filin yaƙi, Volodymyr Zelensky ya ƙaddamar da yaƙi na zance a kan biranen ƙasashen Turawan Yamma.
Ya yi wa majalisar ƙasashe 10 jawabi cikin mako biyu, inda yake samun tafi da jinjina a kodayaushe.
Kai-tsaye ta bidiyo daga Kyiv babban birnin ƙasarsa da aka yi wa ƙawanya, sanye da koriyar riga, yakan ƙare jawabin nasa a lokuta da dama da dunƙulallen hannu. Yayin da ake tsaka da tafi, sai ya ɓace kawai. Mutum ne cikin gaggawa da ke da abubuwa a gabansa.
"Ya san yadda zai tallata kishin ƙasa," a cewar Jonathan Eyal na cibiyar Royal United Services Institute. "Ba a jawabi ba kawai, har ma shigarsa, a bangon bayansa, da kuma inda yake maganar."
Yi wa Turawa tsawa
Jawaban nasa, waɗanda ya fara da bayani ga 'yan majalisa a Landan ranar 3 ga watan Maris, na da wani ƙudiri ɗaya na gaggawa - don tattara goyon bayan ƙasashen - kuma Zelensky ya ci gaba da yin jawabin ta hanyar isar da saƙon.
Daga faɗuwar Bangon Berlin zuwa harin 9/11 a biranen New York da Washingto, Mista Zelensky ya sha taɓo batutuwan da suka faru da ƙasashe marasa daɗi.
A birnin Paris na Faransa a ranar Laraba, ya taɓo maganar "liberté, égalité, fraternité". A Japan, ya taɓo batun bala'in nukiliya.
Mista Zelensky ba ya ɓata lokaci wajen isar da saƙonsa. Cikin minti ɗaya ko biyu da fara jawabinsa a Landan, sai ya fara kwatanta yaƙin Ukraine na kwana 13 da Yaƙin Birtaniya, wanda aka yi lokacin Yaƙin Duniya na Biyu.
"Ya kamata mu fafata a dazuka, a filaye, a gaɓar ruwa, a birane da ƙauyuka, a kan tituna, za mu fafata a kan tsaunuka," in ji shi.
Amma yayin da yake ƙara faɗaɗa jawabansa zuwa majalisu, wasu abubuwa sun bayyana a jawaban nasa. Ba ya jin tsoron yi wa Tuarawan tsawa saboda abin da ya kira gazawarsu wajen ba shi taimakon da ya dace.
Ƙarfin kunyatarwa
"A kowane jawabi, yakan ce ku waɗanne irin mutane ne?" a cewar Nomi Claire Lazar, wata farfesa a sashen hulɗa da ƙasashe a Jami'ar Ottawa. "Wace irin ƙasa ce ku? Idan kuka kasa gane abin da ke faruwa to Allah-wadaranku."
Cikin jawabin da ya yi wa majalisar Amurka cike da ambato Pearl Harbour da Martin Luther King da Mount Rushmore, Shugaba Zelensky ya faɗi wasu abubuwa da suka saɓa wa harkokin difilomasiyya ƙarara. "Mun nemi martani," in ji shi. "Martani ga ayyukan ta'addanci. Wannan wata babbar buƙata ce?"
Da yake jawabi ga majalisar Italiya ranar Talata, Shugaba Zelensky ya sake ɗauko batun kunyata masu sauraron nasa, yana mai cewa abokan Shugaban Rasha Putin na yawan zuwa Italiya hutu.
"Kar ku zama matattarar masu kisa," kamar yadda ya tsawatar musu.
A matsayinsa na shugban ƙasar da ke fuskantar yaƙin da ba ta tsokana ba, Farfesa Lazar ta ce Mista Zelensky na da damar yin hakan. "Ba zai yiwu ka je wata majalisar ƙasar waje ba ka ce Allah-wadaranku," in ji Farfesa Lazar. "Sai dai fa idan kana da matsayin mai shiga tsakani."
"Ina ganin akwai ɓacin rai a ransa da tawagarsa," a cewar Orysia Lutsevych na cibiyar Chatham House. "Gani suke har yanzu mutane ba su damu ba sosai."
Tafi da jinjina
Cikin kowane jawabinsa, wanda mai taimaka masa Dmytro Litvin ya taya shi rubutawa, Zelensky na kama hankalin masu sauraronsa; 'yan siyasa na kaɗuwa da kalamansa da waɗanda ba a saba jinsu ba a siyasance da kuma yadda suke shugaban ke furta su cikin ɓacin rai.
Amma kuma yana magana ne saboda mutanensa waɗanda kuma suke sauraronsa.
Yana magana da harshen Ukrain kuma ba ya saka kwat da aka saba ganin 'yan siyasa da ita. An samu babban sauyi kan ɗan siyasar da farin jininsa ke raguwa 'yan watanni kafin fara yaƙin.
Kafin fara yaƙin, matsayin Mista Zelensky na ɗan wasan barkwanci nauyi ne kan 'yan Ukraine. Amma da aka kawo musu hari, sai hakan ya zama kadara.
"'Yan wasan barkwanci na samun kuɗinsu ne ta hanyar shiga tunanin masu sauraronsu," in ji Farfsa Lazar. "Irin wannan abin ne ke sauya mana tunani. Yana sa mu mu ji daɗi. Yana sa mu dariya."
Sauya tunani
Babban dalilin yin jawaban kenan. Mista Zelensky bai fara yi wa majalisun jawabi ba kawai saboda ya nemi su tausaya wa ƙasarsa. Ukraine na fafata yaƙin tabbatuwarta, kuma za ta ci gaba da yin hakan ne kawai tare da taimakon kayan yaƙin da ƙawayenta za su ba ta.
Ya shafe makonni yana roƙon ƙungiyar ƙawancen tsaro ta Nato ta saka dokar hana tashin jirage a Ukraine wato no-fly zone. Ya san ba zai samu hakan ba. Amma zai iya samun wani abin daban mai amfani.
"Ina ganin suna cewa babu maganar no-fly zone, amma idan babu to me za su bayar a madadinta?" in ji Ms Lutsevych. "Ina ganin salon kenan."
A ranar Talata, shugaban ma'aikatan Zelensky, Andriy Yermak, ya gabatar da abin da zai maye gurbin no-fly zone. "Muna roƙonku ku saka no-fly zone ko kuma ku ba mu makaman kare sararin samaniya," a cewarsa.
Tuni aka fara shirin ƙarfafa tsaron samaniyar Ukraine, kuma Amurka na tunanin ba da tsofaffin makamai da aka ƙera lokacin Tarayyar Soviet amma har yanzu suna aiki.
Jonathan Eyal ya ce salon da Mista Zelensky ke bi yana aiki.
Yayin da shugabannin Turai ke tattaunawa game da yaƙin, "maudu'in shi ne waɗanne irin makamai za a ba shi," a cewarsa.