Mun bi ƙa'ida wurin tsige Mahdi Gusau – Kakakin Majalisar Zamfara

An wallafa

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara a Najeriya, ya yi watsi da ce-ce-ku-cen da ake yi na cewa ba su bi tsari ba wurin tsige tsohon mataimakin gwamnan jihar Barrister Mahdi Aliyu Gusau.

Yayin wata hira da BBC, Honarabul Nasiru Mu'azu Magarya ya shaida cewa rashin sanin abubuwan da suka faru ne ya sa wasu ke zargin majalisar da yin ba daidai ba.

Ya bayyana cewa kundin tsarin mulki ne ya ba su dama domin gudanar da bincike don tsige gwamna ko mataimakin gwamna idan sun aikata wani laifi.

Honarabul Nasiru ya ce duk wanda ya soki rawar da majalisa ta taka kan wannan lamari bai fahimci majalisa ba da irin aikin da take yi.

"Majalisar dokokin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancina ta karɓi duk abubuwan da ya kamata ta karɓa kuma ta bi tsari da kuma dokar da ƙasa da kundin tsarin mulki suka ba mu har aka kai wurin aiwatar da wannan.

"Duk wanda ya bi wannan tsari daidai, bai kamata ya zama abin suka ba sai dai idan ba a fahimci yadda tsarin yake ba," in ji shi.

Tun kafin tsige tsohon mataimakin gwamnan, sai da aka kafa kwamitin bincike domin ya tantance zarge-zargen da ake yi masa, sai dai kwamitin bai ji ta bakin Barrista Mahdi ba har aka tsige shi sakamakon rashin zuwan gaban kwamitin da bai yi ba.

Sai dai a nasa ɓangaren Honarabul Nasiru ya bayyana cewa " abin da tsarin doka ya ce kwamitin na da alhakin ya gayyato shi, idan ya gayyato shi bai samu zuwa ba zai sake ba shi gayyata ta biyu, wanda kuma duka wannan kwamiti sai dai ya yi masa gayyata ta ɗaya da ta biyu.

"Kundin tsarin mulki ya ba kwamitin ƙarfin gaske na cewa idan ya gayyaci wanda ake tuhuma har sau biyu bai zo ba to laifukan da ake tuhumar shi da su sun tabbata domin da ba su tabbata ba da ba zai ƙi zuwa ba," in ji Honarabul Nasiru.

Sai dai a wata hira da BBC ta yi da tsohon mataimakin gwamnan na Zamfara a kwanakin baya, ya ce abin da ya sa ya ƙi zuwa gaban kwamitin saboda umarnin da kotu ta bayar na cewa a tsayar da abubuwa cak a yadda suke.

Sai dai Honarabul Nasiru ya bayyana cewa ba su saɓa umarnin kotu ba domin abin da kotu ta ce a tsaya a kan shi sun tsaya a kan shi inda ya ce wannan wani abu ne na daban