Gane Mani Hanya: Ba gwamnoni ne suka hana ruwa gudu a APC ba - Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar
Latsa hoton sama ku saurari shirin:
Shirinmu na Gane Mani Hanya na makon nan ya tattauna da Gwamna Mohammed Badaru Abubakar na Jihar Jigawa a arewacin Najeriya kan halin da jam'iyyar APC ke ciki.
A Najeriya a yayin da jam’iyyar APC mai mulkin kasar ke shirin gudanar da babban taronta a karshen wannan watan, wani jigo a jam’iyyar ya ce ba suda wani zabi illa bin dan takarar da shugaba Muhammadu Buhari ya ke goyon baya.
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar ya ce babu gaskiya a zargin da ake musu ne cewa wasu daga cikin gwamnonin arewa sun yi kane-kane sun hana ruwa gudu a jam’iyyar ta APC.
A tattaunawa da Editan BBC Hausa Aliyu Abdullahi Tanko, gwamnan ya soma ne da bugun kirji cewa jam’iyyar APC ta taka rawar gani tsawon lokacin da ta shafe a kan mulkin. Sai dai mun naɗi wannan hirar kafin sabuwar ɓarakar da ta kunno kai a APC a farkon wannan makon.