'Ina shan maganin ciwon koda na N35,000 a kowace rana'
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ranar Alhamis ta biyu ta kowane watan Maris ana bikin ranar masu ciwon koda ta duniya.
Ana bikin ne don jan hankalin jama'ar duniya kan girman cutar da matakan da ya kamata a dauka wajen kare kai daga kamuwa da cutar.
Nkwanko Faithful na daga mutane da suke fama da ciwon koda a Najeriya, wacce tace tana shan wahala a jikinta sannan tana fama da wahalhalun kashe kudi wajen neman magani. A cikin wannan bidiyon ta bayyana mana yadda ta kamu da cutar da da kuma yadda take jinyar cutar ta ciwon koda.
Sannan wani kwararren likita ya bayyana girman cutar, da yadda ake kamuwa da ita, da matakan kariya daga cutar ta koda.