Ku San Malamanku tare da Sheikh Musa Adam Mai Hula
An wallafa
Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon.
Sheikh Musa Adam Mai Hula ya ce ya taso ne kawai ya ganshi a makaranta yana karatu ne, inda ya ce ba zai iya tantance yaushe aka saka shi a makaranta ba.
Ya ce ya soma makarantar allo a makarantar Malam Yuguda a garin Numan.
A ɓangaren boko kuma, ya soma ne da makarantar Central da ke garin na Numan inda a nan ya yi firamarinsa.
Bayan mahaifinsa ya koma garin Gombe, a nan ma Sheikh Musa inda a nan ma ya yi karatukan addinin musulunci da na boko.
Malamin ya ce duka surorin Al-Ƙur'ani abin so ne ga Musulmi amma ya fi son Suratul Zumar saboda tauhidin da ke cikinta.