Me ya sa Buhari ke jan ƙafa wajen sa hannu a ƙudurin dokar zaɓe?

An wallafa

An fara nuna fargabar cewa mai yiwuwa Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ba zai sa hannu kan sabon ƙudurin dokar zaɓen da aka yi wa garambawul a 2021 ba, duk da kwaskwarimar da Majalisun Tarayya suka sake yi mata.

Ƙasa da mako biyu kacal ya rage wa shugaban ƙasar bayan tun farko ƙudurin dokar ya shafe wata ɗaya curr a hannunsa ba tare da ya yi hakan ba, saboda batun zaɓen fitar da gwani.

Wasu dai na fargabar cewa zaɓen 2023 na iya zama ɗaya daga cikin mafiya rashin inganci a tarihin Nijeriya matuƙar aikin gyara dokokin zaɓen da aka shafe tsawon lokaci ana yi ya tashi a banza.

Ƙudirin dokar zaɓen da aka yi wa garanbawul ta 2021 wadda kuma aka aika wa Shugaba Buhari tun ranar 31 ga watan Janairun 2022, ta cika kwana 15 kenan a ranar Talata 15 ga watan Fabrairun 2022 a fadar shugaban ƙasar.

A bara sai da Shugaba Buhari ya shafe wata guda kafin sanar wa majalisa cewa ba zai sa hannu kan ƙudurin dokar ba. A karon farko batun zaɓen fitar da gwani ne hujjarsa ta ƙin sanya hannu.

Sai dai a wannan lokaci kuma wasu rahotanni na cewa mutanen da suka hura wa waccar wuta sun sake zagayawa inda suke ci gaba da matsa wa Shugaba Buhari lamba.

Bayanan sun ambato masu matsa lambar na ikirarin cewa ƙudurin dokar cike yake da wasu shaɗarori na nuna wariya kuma ba su dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.

Cikin masu nuna damuwa game da wannan jan ƙafa har da irin su Farfesa Jibrin Ibrahim, Darakta a Cibiyar Bunƙasa Harkokin Dimokraɗiyya da Ci gaban Ƙasa wato CDD.

"Abin da ke damunmu shi ne wataƙila suna so su gaya wa shugaban ƙasa ka da ya sa hannu.

"Dalili shi ne ranar Litinin da ta wuce mun ji Ministan Shari'a Malami yana cewa, ko da yake bai karanta ba, amma ya ce idan ya ga akwai son kai a ciki, zai bai wa shugaban ƙasa shawara kar ya sa hannu.

"To abin mamaki shi ne idan bai karanta ba me ya sa zai ce zai bayar da shawara kar a sa hannu.

"Akwai wani abu da ke baya kenan wanda dai, ko da yake ba mu sani ba, amma akwai jita-jita da yawa da suka ce, ana nan ana kamun ƙafa cewa kar shugaba ƙasa ya sa hannu, dalili shi ne, an ce ministocin da suke so su yi takara su sauka daga muƙamansu.

"Kuma wannan abin ba wani sabon abu ba ne, tun da aka kafa wannan, duk jamhuriyar nan huɗu haka ake yi," a cewar Farfesa Jibrin.

Martanin Shugaba Buhari

Shi kuwa mai magana da yawun shugaban Nijeriya Malam Garba Shehu cewa ya yi ƙudurin dokar zaɓen har yanzu yana gaban Shugaba Buhari, kuma yana nazari a kansa, "don tabbatar da yin adalci a ƙasa da su kansu al'ummar ƙasa.

"Duk abin da za a yi za a tabbatar da cewa ci gaba zai kawo ba tawaya zai kawo ga ƴanci ko ga ƙasa ba.

"Haƙiƙa a wancan lokaci abin da ya fi tsone ido shi ne wannan batu da shugaban ƙasa ya gabatar ga majalisa kuma suka amince.

"Amma ga duk wanda yake sa ido ga yadda abubuwa suke gudana a ƙasar na kai da komowarsu, suna jin irin sa'insar da ake yi a ce wannan a ce wancan

"Ba so nake na ce maka zai sa hannu ko ya ƙi sa hannu saboda abubuwan da ke ta tasowa yau da gobe a kan wannan batu ba.

"Wannan ya dogara kan irin shawarwarin da ya samu musamman daga ministansa na shari'a da kuma ɓangaren shari'a da ita kanta hukumar zaɓe.

Masu nuna fargabar dai sun ce matuƙar Shugaba Buhari ya ƙi sa hannu a karo na biyu kan ƙudurin dokar zaɓen da aka yi wa gyarana fuska, hakan zai tilasta wa hukumar zaɓe ta INEC ta karkaɗe tsohuwar dokar zaɓe ta 2010, wadda suka ce tana cike da matsaloli.

Daga cikin matsalolin har da batun wani hukuncin Kotun Ƙoli da ya ce babu hujjar yin amfani da na'urar tantance masu zaɓe, wani lamari da ake ganin na iya kawo gagarumin naƙasu ga zaɓen 2023.