Murmushi da wushirya da rini a wasu zababbun hotunan Afirka na mako: 4-10 February 2022

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna daga faɗin Afirka na wasu abubuwa da suka faru a makon nan:

Short presentational grey line
Africa week

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi daruruwan mutane ne suka halarci bikin Brixton Light Festival, taron da al'umma ke gudanarwa a babban birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Africa week

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar a cikin birnin, wani mai zane ya ƙarasa aikin yi wa zanen da ya yi ado a Kasuwar Victoria Yards.
Africa week

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu ziyara suna yawon bude ido kallon ra'ayoyi a wani wajen tarihi a Khoms da ke arewacin Libya, a ranar Juma'a.
Roman amphitheater

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masoya ƙwallon kafar Masar a birnin Alkahira na cikin halin damuwa yayin da kasarsu ke buga wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika da Senegal...
Roman amphitheater

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kungiyar Lions of Teranga ta kasar Senegal ta samu nasara a wasan da ci 4-2 a bugun fenareti, lamarin da ya janyo murna da farin ciki a Dakar babban birnin kasar...
Roman amphitheater

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gasar cin kofin AFCON da aka yi a daren Lahadi, shi ne na farko da Senegal ta ci nasara, wanda hakan ya sa aka ji dadi sosai.
Roman amphitheater

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata ne yara suka fita kallon barnar da guguwar Batsirai ta yi a Madagascar, inda akalla mutum 92 suka mutu, sannan sama da gidaje 91,000 suka lalace.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mutane suna kashe wutar a gandun dajin Aberdare a kasar Kenya ranar Litinin. Har yanzu ba a san abun da ya haddasa gobarar ba, wadda aka dauki kwanaki biyu ana kashewa.
Roman amphitheater

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Haka kuma a ranar Litinin, abin sha'awa ƴan yara da giɓinsu sun daddage suna karatun Islamiyya a wata makaranta da ke Maiduguri a Najeriya.
Roman amphitheater

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar, a arewacin Maroko ne mutane suka shiga cikin damuwa yayin da masu ceto ke kan ceto wani yaro dan shekara biyar da ya fada a rijiya kwanaki kadan da suka wuce...
Raya Oram

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kokarin ceto Rayan Oram ya ɗimauta al'umma da jama'ar duniya. Abun bakin cikin shi ne bai rayu ba. Wasu sun yi ta kunna kendira domin karrama shi na ranar Litinin.
Africa week

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mutum a Tunisia na amfani da launin dodon kodi da ya samo a teku don rina tufafi zuwa launin ruwan goro, ta hanyar bin wani tsari da Phoeniciyawa suka fara yi sama da shekaru 2,000 da suka wuce.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Washe gari a Kenya ne aka fara shuka fure a saman ginshikan babban titunan Nairobi...
Africa week

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu sun yaba da koren launin - sai dai masu kare muhalli sun damu da tasirin da ginin zai yi wa muhalli. Kuma an bar mutum 40,000 cikin damuwa bayan da aka rusa gidajensu domin gina wannan katafaren ginin.

Dukkan hotunan suna da haƙƙin mallaka.