...Daga Bakin Mai Ita tare da Ladin Cima Haruna

Bayanan bidiyo, ...Daga Bakin Mai Ita tare da Ladin Cima
An wallafa

Ku latsa hoton sama domin kallon bidiyon:

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 85 din, shirin ya tattauna da fitacciyar ƴar wasan Hausa, wadda ke fitowa a matsayin uwa ko kuma kaka a masana'antar Kannywood wato Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya.

Ta bayyana cewa ta soma harkar fim bayan rasuwar mijinta inda ta ce dama tun a baya tana da sha'awar fim din. Ta ce Kaduna suke zuwa su yi fim saboda a zamanin babu gidan talabijin a Kano.

Ta bayyana cewa ta soma fim tun zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gowon.

Ta bayyana cewa ta yi aiki a asibiti kuma zamanin Kabiru Gaya na gwamnan Kano ne ya ɗauke su aikin asibiti amma a yanzu ta yi ritaya.

A cewarta, a tsawon lokacin da ta ɗauka tana fim, ba ta yi fim din da za a ɗauko dubu ashirin ko talatin ko hamsin a bata ba inda ta ce ana biyanta daga dubu biyu zuwa dubu biyar idan ta yi fim.

Ta ce a zamanin, ba a biyansu kuɗi, amma saboda sha'awar fim ɗin, suna ƙagara ranar Juma'a ta zo su tafi yin fim ɗin idan sun kammala sai Lahadi su koma Kano.