Hanyoyi uku da aka fi yi wa mutane kutse a intanet

Bayanan bidiyo, Hanyoyi uku da aka fi yi wa mutane kutse a intanet
An wallafa

Ana samun ƙaruwar mutanen da suke faɗawa tarkon miyagu masu yi wa kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane kutse akowane lokaci.

Wani bincike da da wani kamfanin tsaro ya fitar ya nuna cewa a watan jiya kadai an ringa yunƙurin karɓe iko da shafukan wasu kamfanoni har sau miliyan 20 akowce rana.

Shafukan mutanen da aka ringa yi wa yunƙurin kutsen sun haɗa da kamfanoni kamar su Amazon, da eBay, Intagram da Facebook.

Ga wasu manyan hanyoyi uku da ake yi wa mutane kutse da kuma hanyoyin da za ku kare kanku.