Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Sulaiman Sulaiman

An wallafa

Sheikh Muhammad Sulaiman Sulaiman asalin ɗan Gombe ne amma akasarin rayuwarsa ya yi ta ne a garin Jos na Jihar Filato. Haka kuma akasarin karatun da malamin ya yi, ya yi sa ne a garin na Jos.

Malamin ya soma karatunsa na firamare a wata makaranta da ke wani ƙauye mai suna Umoko a Jihar Ribas da ke kudancin Najeriya. Bayan malamin ya kammala firamarensa sai ya kuma yi sakandare inda ya yi H.I.S wato Higher Islamic Studies a wancan lokaci inda ya yi karatun a garin Jos.

A lokacin da yake karatun na H.I.S, Sheikh Sulaiman ya haɗa abu biyu a lokaci guda inda ya rinƙa karatu a Arabic Teachers College Grade 3.

Bayan ya kammala, sai da taimakon Sheikh Musa Ibrahim Sagagi Malam Muhammad ya samu gurbin karatu a kwalejin ilimi ta Kano.

Malam ya shafe shekara uku yana karatu a kwalejin ilimi ta Kano inda ya samu takardar shaidar karatu ta NCE, inda a cewarsa, daga kansu aka soke yi wa ƙasa hidima ga waɗanda suka kammala NCE wanda hakan bai bar su sun yi NYSC ɗin ba.