An yi ganawar tarihi tsakanin Isra'ila da Falasdinu

An wallafa

Shugaban gwamnatin Falasdinawa Mahmoud Abbas ya gana da ministan tsaro na Isra'ila Benny Gantz a yankin Isra'ila, a ziyararsa ta farko a can cikin shekara sama da 10.

Ganawar mutanen biyu ta tsawon sa'a biyu da rabi ta kasance ne a gidan Benny Gantz da ke Rosh Haayin a kusa da Tel Aviv.

Wani jami'in Falasdinawa ya ce sun tattauna ne kan muhimmancin yadda za a samar da yanayin da zai kai ga samun mafita ta siyasa ga rikicin Isra'ila da Falasdinu.

Mista Abbas da mai masaukin nasa, ministan tsaron na Isra'ila sun kuma tattauna a kan zaman dar-dar da ake ciki a yankin Gabar Yamma ta tekun Jordan dangane da gidajen Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna da sauran batutuwa na tsaro da tattalin arziki da kuma na ayyukan jin-kai.

Wannan dai ba ita ce ganawarsu ta farko ba, domin sun taba tattaunawa a watan Agusta lokacin da Gantz ya je Ramallah a yankin da Isra'ila ta mamaye a Gabar Yamma, inda a can ma suka tattauna a kan tsaro da batutuwan da ba su shafi tsaro ba da na tattalin arziki.

A lokacin ministan tsaron na Isra'ila ya gaya wa Mahmoud Abbas cewa Isra'ila na son karfafa tattalin arzikin Falasdinu.

Duk da cewa ita wannan ganawa ba wai ta nuna wata nasara da aka samu ba ne ta kyautata dangantaka tsakani, to amma ko ba komai ta nuna cewa manyan jiga-jigan biyu a rikicin, suna ganin har yanzu tattaunawa na da muhimmanci a tsakaninsu.

Shugaban Amurka Joe Biden yana son bangarorin biyu su gyara dangantakar da ke tsakaninsu wadda ta kara tabarbarewa tun zagaye na karshe na tattaunawar gaba da gaba ta zaman lafiya da ta wargaje a 2014.

Mista Biden a lokacin ya bukaci Firaministan Isra'ilar Naftali Bennett da ya dauki matakai na inganta rayuwar Falasdinawa wadanda su ne a tsakiyar rikicin, tare da tallafa wa duk wata babbar dama ta tattalin arziki gare su.

Falasdinawan da gwamnatin Amurka ta lokacin Trump ta kawar da kai daga kansu, tare da daukar wasu matakai na muzguna wa muradunsu - amincewa da Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila da mayar da ofishin jakadancin Amurka birnin daga Tel Aviv.

Shugaban na Amurka ya tabbatar da matsayarsa ta cewa tattaunawa ta samar da kasashe biyu ita ce hanya daya tilo mafi muhimmanci wajen cimma zaman lafiya mai dorewa a rikicin na Yahudawa da Falasdinawa.

Hukumar Falasdinawa ta saba tsakaninta da Isra'ila a shekarar da ta wuce a kan shirin tsohon Firaminista Benjamin Netanyahu na mamaye wani babban yanki na Gabar Yamma, wanda Falasdinawa suke so a matsayin kasarsu mai 'yancin kai tare da Gaza.

Sai dai bangarorin biyu sun maido da alaka a watan Nuwamba bayan dakatar da wannan shiri na mamaya, kuma dadin dadawa Mista Bennett mai ra'ayin rikau ya maye gurbin Netanyahu a matsayin Firaminista, inda ya kafa gwamnati ta hadaka da ra'ayin kawo sauyi, da masu tsakatsakin ra'ayi da Larabawa da sauran jam'iyyu masu ra'ayin rikau.

Mista Bennet wanda ya yi watsi da batun kafa kasar Falasdinu kafada da kafada da Isra'ila, ya ce gwamnatinsa ta hadaka ba za ta yi mamaya ba, ba kuma za ta yi yarjejeniyar zaman lafiya da Falasdinawa ba a lokacin.