Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yahudawa za su shiga unguwar Musulmai a macin da za su yi a birnin Kudus
Gwamnatin Isra'ila da ke shirin barin mulki ta amince wa masu ra'ayin addini 'yan kishin kasa su gudanar da gangami wanda a baya aka soke bisa tsoron abin da masu shirya shi suka ce haddasa sabon rikici.
An shirya cewa masu macin za su bi ta Unguwar Musulmai da ke Birnin Kudus ranar Alhamis, amma 'yan sanda sun ki amicewa da tsarin nasu na farko.
Yanzu za a yi macin ranar Talata.
Hamas, kungiyar Musulmai da ke iko da yankin Gaza, ta yi barazanar tashin hankali idan aka gudanar da gangamin.
Akalla mutum 242 aka kashe a Gaza sanna aka kashe mutum 13 a Isra'ila a rikicin da aka kwashe kwana 11 ana tafkawa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa a watan jiya.
Majalisar ministoci ta Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ce ta yanke shawarar bayan wani taro ranar Talata.
Majalisar dokokin Isra'ila, Knesset, za ta kada kuri'a kan kafa sabuwar gwamnati ranar Lahadi. Gwamnatin Mr Netanyahu, firaiministan Isra'ila da ya fi dadewa a kan mulki, tana fuskantar kawo karshen wa'adinta idan majalisar ta amince da sabuwar gwamnatin hadin gwiwa.
Idan hakan ya tabbatar, nauyin bayar da umarnin yin gangamin zai rataya a wuyan sabuwar gwamnatin da Naftali Bennett da Yair Lapid, za su jagoranta, kwana biyu bayan sun soma mulki.
Bisa al'ada ana gudanar da macin Ranar Kudus a kowace ranar 10 ga watan Mayu kuma hakan yana tunawa da ranar da Isra'ila ta kwace Gbashin Kudus - wanda ke kunshe da Tsohon Birni da wurare masu tsarki - a Yakin Gabas Ta tsakiya da aka yi a 1967. Daruruwan matasan Yahudawa ne rike da tutoci suke ficewa ta Unguwar Musulmai zuwa Kofar Damascus, suna wakokin kishin kasa.
Falasdinawa da dama suna kallon hakan a matsayin tunzaru domin neman rikici.