Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan ziyarar Shugaba Buhari a jihar Borno
An wallafa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis.
Shugaban ya samu tarba daga 'yan jihar, duk da rahotannnin cewa mayakan kungiyar ISWAP sun tayar bama-bamai a wurare da dama, yayin ziyarar shugaban.
Ana sa ran shugaban zai karɓi rahoto daga jami'an rundunar sojin Najeriya da ke faɗa da Boko Haram
Haka kuma shugaban zai ƙaddamar da wasu manyan ayyukan da gwamnatinsa da ma gwamnatin jihar suka yi a jihar.
Ga wasu hotunan ziyarar shugaban kasar: