Hotunan masu wasan wuta da yan rawa a bikin al'adu na Senegal

Two men with white face paint on, wearing elaborate lion-like head dresses and colourful accessories.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Men dressed as lions for the parade
An wallafa
1px transparent line

Masu wasan haɗiyar wuta, da waɗanda suka sha zane a fuskokinsu da masu tafiya a kan sanduna sune suka mamaye bikin raya ala'di na Senegal da ake kira da Great Carnival of Dakar na biyu.

Bikin wanda ake yi daga ranar Juma'a zuwa Lahadi yana kamawa ne a mako na ƙarshe a watan Nuwamba kuma lokacin bikin kan yi daidai da lokacin da masu yawon bude ido ke zuwa kasar ta Senegal.

Senegal dai ita ce kasar da masu yawon bude ido suka fi zuwa a yankin yammacin Afirka, amma a yanzu kasar na fama da annobar cutar korona, a cewar shafin inatent na Africanews.

Kasar ta samu halartar masu yawon bude ido 1,376,000 a shekarar 2017, a cewar alkaluma daga Babban Bankin Duniya.

Daya daga cikin maƙasudin wannan bikin shi ne nuna wa mutane a duk fadin duniya irin al'adun da Senegal take da su.

Taken bikin na wannan shekarar shi ne "Labaran jarumai a Senegal da kuma wasu wurare", wanda aka samo daga cikin al'adun kasar.

An gudanar da gagarumin gangami inda aka yi baje kolin al'adun kasar a cikin kwanaki biyu na ƙarshen mako.

1px transparent line
A woman dressed in white smiling and holding her hand out

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gangamin ya nuna kayan gargajiya da kuma raye-raye da kuma wakoki
Women dancing dressed in white with beaded head dresses. The woman in the middle is dancing and smiling

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Waɗannan matan kabilar Diola na sanye da kayansu na gargajiya
1px transparent line

Bikin wanda aka ɗaga a shekarar da ta gabata saboda annobar cutar korona, na bada fifiko kan rawa da waƙoƙi da kuma kayan gargajiya, a cewar jaridar Senegalese paper Le Quotidien.

Daya daga cikin abubuwan da bikin ke mayar da hankali kai shi ne murnar abin da 'yan Senegal ke kira ruhin "teraanga".

Kalmar Wolof na nufin kyautatawa da karamci.

1px transparent line
A man dressed as a lion eating fire

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kaya masu ado sosai na cikin abubuwan da aka saba gani a bikin
1px transparent line

Jami'an gwamnati da dama sun halarci taron buɗe bikin a ranar Juma'a, cikinsu har da ministan lafiya na kasar da magajin garin birnin da kuma ministan gundumomin al'ummu.

Bikin na ƙoƙarin haska al'adu da kuma ƙimar ƙasar tare da kuma haɓaka tattalin arzikin ƙauyuka a cewar wasu jami'ai.

In a July news conference the festival was described as "an economic opportunity for participants" by a representative of the carnival, Fatou Kassé Sarr.

A yayin wani taron manema labarai da aka yi a watan Yuli, an bayyana bikin a matsayin "dama ta samun kuɗi ga masu ruwa da tsaki a harkokin bikin," in ji daya daga cikin masu shirya bikin, Fatou Kassé Sarr.

1px transparent line
A woman having her face painted. She is wearing a traditional head dress and has on red face paint on her eyelids and red paint on her lips

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana yi wa wannan matar zane a fuskarta kafin a fara bikin
A child getting is face painted by another child.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Bikin wuri ne da mutane ke zuwa da iyalinsu
1px transparent line

Waɗanda ke shirya bikin sun bayyana cewa bikin wuri ne da mutane ke zuwa da iyalansu kuma kowace ƙabila ko masu yawon buɗe ido za su iya zuwa ba tare da sun biya komai ba.

Two stilt walkers wearing colourful clothing with a crowd behind them

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yadda masu rawa suka nuna bajintarsu a bikin
Two men wearing colourful traditional clothing singing and smiling

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, These Lebou people are singing during the parade Wasu ƴan ƙabilar Lebou yayin da suke rera waƙoƙi a wajen bikin

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Dukkan hotunan suna da haƙƙin mallaka