Davido: Mawaƙin ya ce masoyansa sun tara masa kusan naira miliyan 175

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Fitaccen mawaƙin Najeriya Davido ya ce masoyansa sun tara masa kusan naira miliyan 175 bayan ya nemi su tara masa kuɗin.

Mawakin ya roƙi masoyansa ne idan har sun yi imani da "akwai waƙarsa da ta yi masu daɗi su tura masa kuɗi," tare da bayyana suna da kuma asusunsa na banki.

Davido ya wallafa hoton yawan kuɗin da ya tara tsakanin Laraba zuwa Alhamis da suka kai kusan naira miliyan 175.

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin mawakin amma har yanzu bai bayar da amsa ba.

Davido - yana ɗaya daga cikin mawaƙan Afrika da ke tashe a duniya. Yana da mabiya miliyan 21.9 a Instagram.

Mawaƙin ya faɗa a Twitter cewa manufarsa shi ne masoyansa da abokan arziki su tara masa naira miliyan 100 domin ya fitar da motarsa ƙirar Rolls Royce daga tashar ruwa a Najeriya don ya biya harajin motar da aka turo masa daga ƙasashen waje.

Yayin da wasu abokansa suka tura masa kudin wasu kuma sukar mawakin suka yi.

Wani mai amfani da Twitter ya ce "Duniya ta haukace, ta yaya Davido zai roƙi masoyansa su tara masa kuɗi?"

Amma wasu na ganin ya cancanta: "Ya cancanci fiye da haka ma.. ya kasance abin alfahari ga mutane da dama. Muna maka murnan zagoyowar ranar haihuwarka @davido."

Wasu da dama sun ta taya mawakin yaɗa kuɗaden da ake tura masa.

Davido ya sha wallafa hotunansa a Instagram cikin motocin alfarma da kuma jirgin sama kuma cikin yanayi na tsadar rayuwa.

A watan Mayu Davido ya bayar da ladar dala dubu goma na kuɗinsa a gasar da ya ƙaddamar da rawa da waƙa a Instagram.