FW de Klerk: Farar fata na karshe da ya shugabanci Afirka Ta Kudu ya mutu

An wallafa

FW de Klerk, tsohon shugaban Afirka Ta Kudu kuma farar fata na karshe da ya jagoranci kasar, ya mutu yana da shekaru 85.

Mr de klerk, wanda jigo ne a yunkurin kasar na komawa turbar dimokuradiyya, an gano ya kamu da cutar daji a wannan shekarar, a cewar mai magana da yawunsa.

Mr de Klerk ya shugabanci kasar daga watan Satumbar 1989 zuwa watan Mayun 1994.

A shekarar 1990 ne ya bayyana cewa zai saki shugaban masu rajin yaki da mulkin wariyar launin fata Nelson Mandela, lamarin da ya kai ga yin zabe mai jam'iyyu da dama a shekarar 1994.

Wata sanarwa da Gidauniyar tsohon shugaban kasar FW de Klerk ta fitar ranar Alhamis da safe ta ce: "tsohon shugaba FW de Klerk ya mutu cikin lumana a gidansa da ke Fresnaye (Cape Town) da sanyin safiya bayan ya yi fama da cutar daji ta huhu."

"Ya bar matarsa e Elita, da 'ya'yansa Jan da Susan da kuma jikokinsa," in ji sanarwar.

Gidauniyar ta ce a watan Yunin wannan shekarar aka gano yana dauke da cutar.

A watan Fabrairun 1989 ne FW de Klerk ya karbi jagorancin jam'iyyar National Party daga wurin PW Botha kuma shekara daya bayan haka ya sanar da dage haramcin da aka yi wa jam'iyyu na shiga zabe ciki har da jam'iyyar Mr Mandela ta African National Congress (ANC).

Matakin da ya dauka ne ya taimaka wajen kawo karshen mulkin wariyar launin fata a Afirka Ta Kudu, kuma ya zama daya daga cikin mataimakan shugaban kasa biyu bayan zaben 1994 wanda Mr Mandela ya yi nasara.

A shekarar 1993 shi da Mr Mandela suka samu kyautar Nobel kan Zaman Lafiya.

An haifi Mr de Klerk a watan Maris na shekarar 1936 a birnin Johannesburg.

Ya yi aiki a matsayin lauya sanna ya rike mukamin ministoci kafin ya maye gurbin PW Botha a matsayin shugaban jam'iyyar National Party a watan Fabrairun 1989.