Taron jam'iyyar PDP cikin hotuna

An wallafa

Ana ƙoƙarin fara jefa ƙuri'a a zaɓen shugabancin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya yayin da ake sa ran zaɓar mutane a muƙamai daban-daban.

Ku biyo mu a nan: Yadda taron PDP ke gudana don sanin abin da ke faruwa a wurin.

PDP

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Taron na gudana ne a dandalin Eagle Square da ke Abuja
PDP

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Ana ƙoƙarin fara jefa ƙuri'a
PDP

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Ana sa ran za a zaɓi kashi 99 cikin 100 na shugabannin ta hanyar sasantawa
PDP

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Mukamai uku ne kawai ake da jayayya a kai ya zuwa yanzu waɗanda ka iya kai wa a jefa ƙuri'a a kansu
PDP
Bayanan hoto, Muƙaman su ne: Mataimakin shugaba na arewa da mataimakin shugaba na kudu da kuma shugaban matasa
PDP

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Shugabannin kwamitin shirya zaɓen na zagayawa domin tabbatar da cewa shirin ya tafi yadda ya kamata
PDP
Bayanan hoto, Wakilan jihohin Abia da Adamawa da Anambra ne za su fara kaɗa ƙuri'asu, inda sauran za su biyo baya.