Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Shettima Habib
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hira da Sheikh Shettima Habib
Fitaccen malamin addinin musuluncin a Najeriya Sheikh Shettima Habib, ya ce duk da bai yi karatun boko ba amma ya taimaka wa masu bincike a cibiyoyin ilimi a Ingila da Jamus, musamman kan babban aikin fassara Al Kur’ani mai tsarki zuwa harshen Kanuri.
Ya ce ya je Ingila sau uku kuma turawan ƙasar da suka yi wa Najeriya mulkin mallaka ne suka gayyace shi zuwa Landan.
Malamin ya ce ya taimaka masu kan binciken da suke yi a kwalejin nazarin zamantakewar kasashen gabashin duniya da na Afrika wato School of Oriental and African Studies da ke tsakiyar Landan.
Ya kuma kai ziyara Jamus sau shida kan aikin fassarar Al Kur’ani mai tsarki da harshen Kanuri a Jami’ar Hamburg.
Tarihin rayuwarsa
Malamin ya shaida wa BBC cewa an haife shi ne a watan Afrilun shekarar 1959 a cikin garin Maiduguri.
Malamin ya ce cikakken sunansa shi ne Shettima Habib ibn Shetimma Ali Shetima Ibrahim.
Ya ce tsawon shekara 23 yake limanci a babban masallacin Juma'a na GRA a Maiduguri.
Kuma malamin ya ce ya gaji limanci ne daga kakansa wanda Shehu Garbai Kakan shehun Borno na yanzu ya naɗa wanda ya haifi babansa.
Sheikh Shettima ya ce yana da shekara bakwai ya fara karatun Kur'ani mai tsarki a gidansu wurin Malam Abdu.
Ya ce yana da shekara 15 zuwa 16 ya haddace Kur'ani. Kuma cikin shekara bakwai ya ce ya sauke tafsirin Kur'ani.
Malamin ya ce ya yi karatu hannun malamai da dama a Borno. Ya yi karatun Tajwidi a wajen Goni Darma.
Sheikh Shettima ya ce lokacin da ya haddace Kur'ani ne ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa saboda irin girman shagalin da aka yi a lokacin.
Kuma rashin mahaifinsa kuma malaminsa ne abin da ya fi bakanta masa rai a duniya.
Abincin da Sheikh ya fi so
Shehun malamin ya shaida wa BBC cewa ya fi son shinkafa da jar miya da kuma tuwo da miyar kuka da man shanu
Iyali
Malamin ya ce matarsa ɗaya kuma yana da ƴaƴa shida, biyu maza hudu mata. Biyu daga cikin matan sun yi aure, biyu kuma sun kammala karatu, a cewar Malamin.
Babban burin malamin shi ne samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Borno da Najeriya baki ɗaya.