Ku San Malamanku tare da Sheikh Umar Usman Ahmad

An wallafa

Wani babban malami a birnin maidugurin jihar Borno a arewacin Najeriya ya ce ba shi da burin da ya wuce ya ga an koma harkokin noma da sauran al'amura a cikin al'ummarda.

Malam Umar Usman Ahmad ya bayyama hakan ne a shirin Ku San Malamnku na BBC Hausa.

Malam ya ce yana jin takaicin yadda rikici ya mayar da jihar Borno baya a fannoni da dama tare da durkusar da al'amura tsaown lokaci.

An shafe shekaru ana fama da rikicin Boko Haram a jihar, wadda a baya cibiya ce ta abubuwan ci gaba da dama a kasar.

Wane ne Malam Umar?

An haifi Malam Umar Usman Ahmad a karamar hukumar Jere da ke Jihar Borno a shekarar 1983.

Ya fara karatunsa a garinsu tun daga Suratul Fatiha har ya sauke a wajen malamai daban-daban.

Sannan ya yi karatun sauran littattafai a wajen wasu malaman.

Ya ce har yanzu yana karbar karatun litattafai a wajen malamai daban-daban.

Ya yi karatun zamani a High Islam inda ya kammala sakandare.

Malamin ya kuma halarci makarantar An-Nahda ta Sheikh Ibrahim Saleh.

Ya yi difloma a Kwalejin Muhammad Gwani ya karanta Larabci da Addinin Musulunci.

Malam ya yi digiri a Jami'ar Maiduguri a kan Islamci Studies.

Ya zarce da digiri na biyu a wata jami'a a Jamhuriyyar Nijar.

A yanzu haka malam yana karatun digirin digirgir a Sudan, kuma yana koyawar a Kwalejin Muhammadu Gwani.

Surar da malam ya ce ta ba shi wahala lolacin da yana koyo a cikin a-Kur'ani ita ce Jinn.

Sannan ya ce Suratu Yusuf na sa masa nutuswa sosai.

Abin farin cikin da ba zai manta da shi ba shi ne lolacin da aka nada dhi limamin Masallacin Al-ansar. Sannan kuma yana so ya ga yana taimaka wa mutane.

Amma babban abin da ke sa shi bakin ciki shi ne ya gaza biya wa wani da ya nemi alfarmarsa bukatarsa musamman ta taimakon abinci.

Malam ya ceba abin da ya finso ya ga an magance a yanzu irin a samar da zaman lafiya a Najeriya.

"Ina so na ga al'ummar Birno sun samu zaman lafiya na ga ana walwala a koma harkar noma da sauran abubuwa," in ji shi.

Malam yana da mata uku da 'ya'ya sama da 10.

Karin labarai: