Hotunan Afirka na makon 1-7 Oktoba 2021: Tsalle cikin nishadi da masu tafiya a Sahara

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga Africa da sauran ƙasashen duniya.

Short presentational grey line
Wata tawagar ƴan rawa a dandalin Eagle Square a Abuja Najeriya lokacin shagulgulan cikar ƙasar shekara 61 da samun ƴanci ranar 1 ga watan Oktoba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma'a ƴan Najeriya sun yi murnar cikar shekara 61 da ƙasarsu ta samu ƴanci daga mulkin Burtaniya...
Wannan matar na cikin wasu ƴan rawa da suka yi wasa a Abuja babban birnin Najeriya...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan matar na cikin wasu ƴan rawa da suka yi wasa a Abuja babban birnin Najeriya...
Ƴan Najeriya da dama sun shiga shafin Twitter don aika saƙonni da maudu'in #NigeriaAt61...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ƴan Najeriya da dama sun shiga shafin Twitter don aika saƙonni da maudu'in #NigeriaAt61...
Yayin da wasu ke murna, wasu na zanga-zanga tare da buƙatar Shugaba Muhammadu Buhari ya ajiye aiki.

Asalin hoton, NurPhoto

Bayanan hoto, Yayin da wasu ke murna, wasu na zanga-zanga tare da buƙatar Shugaba Muhammadu Buhari ya ajiye aiki.
Washe gari a Sudan wata tawagar ƴan rawa ta tarbi wasu baƙi a Khartoum.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Washe gari a Sudan wata tawagar ƴan rawa ta tarbi wasu baƙi a Khartoum.
A rana guda a Morocco wata mata na shafa wani raƙumi a jajiberin fara tseren Marathon des Sables - wanda masu shiga tseren ke yin gudun kilomita 250 a hamadar Sahara cikin kwana bakwai...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A rana guda a Morocco wata mata na shafa wani raƙumi a jajiberin fara tseren Marathon des Sables - wanda masu shiga tseren ke yin gudun kilomita 250 a hamadar Sahara cikin kwana bakwai...
Ranar Lahadi an fara tseren a tarin yashin hamada.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Lahadi an fara tseren a tarin yashin hamada.
Ranar Litinin, an taru a Addis Ababa babban birnin Habasha don shgalin rantsar da Firaminista Abiy Ahmed...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin, an taru a Addis Ababa babban birnin Habasha don shgalin rantsar da Firaminista Abiy Ahmed...
Mista Abiy, a dama, ya gabatar da sauye-sauye da dama kuma mulkinsa ya gamu da yaƙin basasa tun bayan hawansa mulki a 2018...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mista Abiy, a dama, ya gabatar da sauye-sauye da dama kuma mulkinsa ya gamu da yaƙin basasa tun bayan hawansa mulki a 2018...
Sai dai masu halartar bikin sun yi murna da farin ciki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sai dai masu halartar bikin sun yi murna da farin ciki.
Idan aka koma Sudan, ranar Talata, wasu mata na tattaki don nuna ƙin jinin wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka sa wa hannu tsakanin gwamnati da ƴan tawaye a 2020.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Idan aka koma Sudan, ranar Talata, wasu mata na tattaki don nuna ƙin jinin wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka sa wa hannu tsakanin gwamnati da ƴan tawaye a 2020.
A birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu kuwa, wata mata ta yi tsayuwar ɗaukar hoto a wani taron masu goyon bayan auren jinsi ɗaya.

Asalin hoton, Gallow Images

Bayanan hoto, A birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu kuwa, wata mata ta yi tsayuwar ɗaukar hoto a wani taron masu goyon bayan auren jinsi ɗaya.
A birnin London kuwa ranar Laraba, ɗan wasan fim Idris Elba da matarsa ƴar asalin Somaliya amma haifaffiyar Canada Sabrina Dhowre Elba mai tallar kayan ƙawa sun halarci bikin haska fim ɗin The Harder They Fall.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin London kuwa ranar Laraba, ɗan wasan fim Idris Elba da matarsa ƴar asalin Somaliya amma haifaffiyar Canada Sabrina Dhowre Elba mai tallar kayan ƙawa sun halarci bikin haska fim ɗin The Harder They Fall.
A Morocco, wannan mutumin na gudu a wasan tseren Marathon des Sables - a rana ta huɗu ta tseren.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Morocco, wannan mutumin na gudu a wasan tseren Marathon des Sables - a rana ta huɗu ta tseren.
A rana guda wani mai sayar da kayan marmari na wucewa ta gaban wani zane da aka yi a kan titi a birnin Johannesburg...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A rana guda wani mai sayar da kayan marmari na wucewa ta gaban wani zane da aka yi a kan titi a birnin Johannesburg...
A birni guda ranar Alhamis masu zanga-zanga sun hau tituna kan manufofin Afrika ta Kudu na tattalin arziƙi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A birni guda ranar Alhamis masu zanga-zanga sun hau tituna kan manufofin Afrika ta Kudu na tattalin arziƙi.
A wani ɓangaren kuwa an jera littafan marubuci Abdulrazak Gurnah ɗan Tanzania a birnin Stockholm bayan da ya lashe lambar yabo ta Nobel ta 2021 a fannin adabi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wani ɓangaren kuwa an jera littafan marubuci Abdulrazak Gurnah ɗan Tanzania a birnin Stockholm bayan da ya lashe lambar yabo ta Nobel ta 2021 a fannin adabi.

Duka hotunan na da haƙƙin mallaka.