eNaira: Abin da ya bambanta kudin intanet na eNaira takardar kudin Naira

eNaira

Asalin hoton, CBN

An wallafa

Babban bankin Najeriya ya kaddamar da shafin intanet na eNaira, a karon farko da kasar ta rungumi amfani da kudin intanet.

A cewar CBN "eNaira zai zama wata hanya mai inganci ta huldar cinikayya da kudin Naira da kasar ke amfani da ita."

Hakan na nufin a matsayin al'umma za su iya amfani da nairar ta intanet wurin sayen kaya a kasuwa kamar yadda ya saba yi da takardar kudin nairar.

Tun da farko CBN ya so kaddamar da shafin na eNaira a www.enaira.com a ranar 1 ga watan Oktoban 2021, wanda ya yi dai dai da ranar samun 'yancin kan Najeriya, amma kuma sai ya sake yanke shawarar samar da shafin kafin lokacin.

A wani sako da babban bankin ya wallafa a shafin ''eNaira zai sa a samu karuwar cinikayya a gida da wajen Najeriya saboda ya fi sauki da sauri da kuma biyan bukata."

To amma tambayar da wasu 'yan Najeriya ke yi ita ce, me ya bambanta Nairar intanet din da wadda ke ajiye a cikin asusun ajiyarsu na banki?

Bambancin eNaira da takardar kudin Naira

A cewar CBN kudin intanet na eNaira babban bankin ne ke da hurumin kula da ita, a maimakon takwararta da ke kwance a asusun ajiya da bankunan yan kasuwa ke iko da ita.

Haka kuma eNaira ba ta da bambanci wurin kadari da nairar da ke asusun ajiya.

CBN ya sanar cewa "amfani da eNaira ya fi riba, ya fi karbuwa, ya fi sauki, ya fi tabbas kuma ita ce hanyar huldar cinikayya da aka fi aminta da ita a wannan zamani."

Me ce ce ribar amfani da eNaira?

Kaddamar da kudin intanet na eNaira na zuwa a dai-dai lokacin da babban bankin Najeriyar ya dakatar da huldar kudin intanet ta cryptocurrency.

To amma CBN ya ce eNaira da ya kaddamar za ta taimaka wurin karfafa tattalin arzikin Najeriya na zamani.

"Amfani da eNaira zai karfafa darajarta da kuma saukaka biyan haraji," a cewar sanarwar ta CBN.

Bugu da kari eNaira ba ta kara kudin ruwa a lokacin hada-hada ba kamar wasu kamfanonin hada-hadar kudin intanet ba.

Me 'yan Najeriya ke cewa?

'Yan Najeriya da dama na bayyana ra'ayoyinsu kan wannan sabon tsari, inda mafi yawa ke maraba da shi.

Watakila ganin cewa dama sun dade da karbar tsarin kudaden intanet irin su Bitcoin, shi ya sa suka yi saurin amsar wannan lamari, kamar yadda masu fashin bakin ke gani.

Kalu Aja @FinPlanKaluAja1 a shafin Tuwita ya ce:

"Babban Bankin Najaeirya CBN zai yi amfani da wani kamfanin kasar waje don zuba jari wajen kaddamar da kudin eNaira. Tambayar da zan sake yi a nan ita ce, shin babu wani kamfanin Najeriya ne da ya cacanta?

"Shi wannan kamfanin kasar wajen ba zai iya hada gwiwa da kamfanin cikin gida ba ne ta yadda CBN zai zuba jarin?"

AvTheSurgeon @Avalldar ma cewa ya yi:

"Ya yi daidai.. wato Najeriya tana son yin amfani da kudin intanet da ake kira eNaira wanda za a fara amfani da shi a hukumance.

"Abin na da ban sha'awa.. kamar akwai ci gaba... duk da dai ina jin kamar hanya ce da gwamnati za ta dinga bin diddigin yadda ake mu'amala da kudi."