Abin da ya sa na yi fim kan fyaɗe a arewacin Najeriya - Salma Phillips
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wata Marubuciya kuma mai ba da umarni Salma Shehu Phillips ta ce mata musamman masu kananan shekaru suna ganin tasku saboda yawan rahotannin fyaɗe da ake samu a yankin.
Salma Phillips, wacce ƴar asalin jihar Kano ce, ta ce ta kaɗu da yawan fyaɗe da ake yi wa ƙananan yara, sannan da yadda waɗanda suka yi fyaɗen ke ci gaba da walwala ba tare da hukunta su ba.
Salma ta ce manufarta ta yin fim ɗin ita ce wayar da kan jama'a da ma duniya su fahimci irin girman matsalar da mata ke ciki, domin a haɗa kai a ɗauki matakin da ya dace.
A yanzu Salam na zaune ne a birnin Ikko na jihar Lagos.