Matar da ta ilimantar da 'ya'yanta 7 daga sana'ar bola a Kaduna

Bayanan bidiyo, Matar da ta ilimantar da 'ya'yanta daga sana'ar bola a Kaduna
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Wani kamfani a Najeriya ya kirkiri sabuwar hanyar samar da inshorar lafiya ga masu karamin karfi ta hanyar karbar tarkacen bolar da suka tara.

Tsarin na Sosocare na karbar tarkacen bolar ne domin sake sarrafa su, a bangare guda kuma su biya wa mai tara bolar kudin asibiti.

Shirin yana samun tallafin Gidauniyar Bill and Melinda Gates.

Fauziyya Kabir Tukur ta ziyarci wata mata, daya daga cikin masu cin moriyar shirin ga kuma bidiyon da ta hada mana daga Kaduna.