Tsohon Shugaban Chadi Hissene Habre ya rasu yana shekara 79

Hissene Habre

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hissène Habré shi ne shugaban Chadi daga 1982 zuwa 1990
An wallafa

Tsohon Shugaban Chadi Hissene Habre ya rasu ranar Talata yana da shekara 79, a cewar Ministan Shari'a na Senegal, Malick Sall.

Mista Habre ya rasu ne a asibiti yayin da yake zaman gidan yari a Senegal bisa aikata laifukan yaƙi da kuma keta haƙƙin 'yan Adam.

Rahotanni sun ce ya rasu ne sakamakon cutar korona.

A lokacin da ya mulki Chadi tsawon shekara takwas, shugaban ya dinga murƙushe 'yan adawa, abin da ya jawo mutuwar mutum fiye da 40,000, a cewar masu bincike.

A shekarar 2016 ne wata kotu ta musamman - wadda ƙungiyar haɗin kan Afirka (AU) da Senegal suka kafa - ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

Ana tuhumarsa da fyaɗe da azabtarwa da bayar da umurnin kisa lokacin da yana kan madafan iko. Amma ya musanta aikata laifukan.

Hissene Habre

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Hissène Habré ya ci gaba da yin tirjiya lokacin shari'arsa

Lokacin shari'arsa, waɗanda suka tsira sun bayar da labarin irin yadda jami'an sirri na gwamnatin Habre suka azabtar da su.

An mayar da ɗaya daga cikin cibiyoyin azabtar da mutane a matsayin wurin ninkaya.

Shedu sun ce an azabtar da mutane ta hanyar amfani da lanarki da ƙunar taba sigari da kuma amfani da gas a idanunsu.

A 1990 ƴan tawaye suka hamɓarar da shi, inda ya nemi mafaka a Senegal.

Bayan shekara 20, kotun Chadi ta zartar masa da hukuncin kisa a bayan idonsa kan laifukan yaƙi.

Lokacin da yake tsokaci game da mutuwarsa, Reed Brody, wanda ya jagoranci gangamin tabbatar da an gurfanar da sohon shugaban, ya ce "Tarihi ba zai taɓa mantawa da ɗaya daga cikin masu mulkin kama karya a duniya da suka kashe mutanensu."

Habre ya ƙwace mulki ne a 1982 bayan haɓarar da Goukouni Oueddei, tsohon ɗan tawaye wanda ya lashe zaɓe.

An ta yin hasashen cewa ya samu goyon bayan CIA, a matsayin babban mai adawa da gwamnatin tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi.

Juyin mulkinsa na ya zo ne a lokacin da ake cikin yaƙi da Libya kan takaddamar fili.

Hibre wanda ya samu goyon bayan Amurka da Faransa, sojojinsa sun kori dakarun Libya a 1983.