Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shan Aspirin 'na iya rage yaɗuwar kansar mama'
- Marubuci, Daga Michelle Roberts
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Edita Kan Harkar Lafiya, BBC News online
- An wallafa
Aspirin na iya taimakawa wajen daƙile cutar kansar mama ta hanyar sa magungunan cutar su ƙara dakile ƙwayoyin cutar masu wahalar magani, a cewar likitoci.
Wata tawaga a Gidauniyar Christie NHS Foundation a Manchester sun fara wani bincike kan masu fama da cutar kansar mama nau'in triple-negative.
Suna tunanin cewa Aspirin na hana kumburi a masu kansar mama.
An gudanar da binciken kan dabbobi kuma an ga sakamako mai kyau.
Mata masu ƙarancin shekaru
Akwai hujjar da ke nuna cewa aspirin na iya taimakawa wajen hana kamuwa da wasu cutukan daji kuma yana rage hadarin yaɗuwarsu.
Amma ya yi wuri a bai wa mutane shawarar fara shan shi. Ana buƙatar ƙarin bincike.
Kusan mata 8,000 ne ke kamuwa da kansar mama nau'in triple-negative a Burtaniya duk shekara - nau'in ba a cika samunsa ba amma yana da wahalar magancewa kuma ya fi shafar mata masu ƙarancin shekaru da baƙaƙen fata.
Wannan cutar ba su da wasu sinadari waɗanda ake kira receptors, haka na nufin wasu magungunan kansar mama kamar herceptin ba za su yi aiki a kansa ba. Ko da yake wasu magungunan na aiki a kansa.
'Tana da matukar wahala'
A binciken, wanda kungiyar agaji ta Breast Cancer Now ta gudanar, za a ba wasu masu fama da cutar aspirin sannan a ba su maganin avelumab kafin an yi masu tiyata da maganin 'chemotherapy.'
Idan aka yi nasara, ana iya gudanar da ƙarin bincike kan aspirin da avelumab kan kansar mama nau'in secondary triple-negative, idan ƙwayoyin cutar kansa suka fara yaɗuwa zuwa wasu sassan jiki.
Beth Bramall mai shekaru 44 da ke Hampshire ta gano tana ɗauke da kansar mama nau'in triple-negative a 2019.
Ta ce: "Babu wata kansa mai sauki amma nau'in triple negative na da matuƙar wahala, kuma ba shi da magunguna da yawa don haka magance shi na da wahala.
"Ciwon nan ya durkusar da ni, ga illolin da ke tafe da shi kamar zubar gashi da tashin zuciya da ciwon gaɓoɓi da ciwon jiki da gudawa da kumburin ciki da jin raɗaɗi a tafukan hannu da ƙafa da ciwon kai mai tsanani da tashi cikin dare lulluɓe cikin gumi da gajiya irin wadda ban taɓa jin irinta ba.
"Na yi dace da jikina ya amshi magungunan.
"Amma waɗannan watanni 18 sun zama masu matuƙar wahala ga ni da iyalina.
"Kuma ina da shekara biyu nan gaba da zan ci gaba da magunguna da hotunan cutar."
Sabuwar hanya
Jagorar masu binciken Dokta Anne Armstrong ta ce: "Ba duka kansar mama ce ke mutuwa idan aka sha magungunan da ke aiki garkuwar jiki ba.
"Gwada amfani da magani kamar aspirin abu ne mai kyau saboda ana samunsa a ko ina kuma ba shi da tsadar samarwa.
"Muna fatan bincikenmu zai nuna haka, idan aka haɗa da magunguna masu aiki da garkuwar jiki, aspirin na iya karfafa ayyukansu kuma ya samar da sabbin hanyoyi masu kyau don magance kansar mama."
Takwararta, Dokta Rebecca Lee ta ce binciken da suka gano a ɗakin gwaji ya nuna cewa aspirin na iya kara ingancin wasu magungunan kansar ta hanyar hana ƙwayoyin cutar samar da sinadaran da ke raunata garkuwar jiki.
"Muna fata aspirin zai dakile kumburi da yaɗuwar cutar yadda garkuwar jiki za ta iya yin aikinta na kashe ƙwayoyin cutar kansa," a cewarta.