Hotunan Afirka na mako 6-12 Agusta: Tsalle-tsalle da fareti da kilisa

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga sassan Afirka ko na wasu ƴan Afirka a wasu wuraren a fadin duniya a makon da ya gabata.

Short presentational grey line
Marcia Alves Lopes yar wasan motsa jikin kasar Cape Verde lokacin da take wasa a gasar olympics a Tokyo, Japan - Juma'a 6 Agusta 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yar wasan motsa jikin kasar Cape Verde Marcia Alves Lopes lokacin da take wasa a Gasar olympics ranar Juma'a.
Shugaban tawagar fareti a Ethiopia ya wulla sandar sa sama a Addis Ababa,Eithiopia- Lahadi 8 Agusta 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban tawagar masu fareti yayin da ya wulla sandarsa sama a wani taro a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia ranar Lahadi.
Mahaya doki sun daga tutar Ethiopia yayin taro a Addis Ababa,Ethiopia - Lahadi 8 Agusta 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mahaya doki rike da tutar Ethiopia suna shawagi a tsakiyar gari.
Wani mutum sanye da kayan al-adar Oromo ya hallaci taron a Addis Ababa , Ethiopia -Lahadi 8 Agusta 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan mutumin sanye da kayan al'adar Oromo ya hallarci taron, wanda da yake goyon bayan sojoji a yain da suke yi da dakaru a arewacin yankin Tigray..
Wani mutum a zaune yayin da wani yake masa aski da reza a sansanin yan gudun hijirar Ethiopia na kabilar Qemant a kauyen Basinga a gundumar Basunda dake yankin gabashin Sudan. Talata Agusta 10, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yakin da ya ɗau watanni tara ya tursasa miliyoyin yan Ethiopia barin muhallinsu, da yawansu sun yi hijira zuwa Sudan. Wadannan yan gudun hijirar da aka dauki hotonsu ranar Talata suna aski, sun fito ne daga kabilar Qemant marasa rinjaye a Amhara mai maƙotaka da yankin Tigray.
Taron mutane Crowds at a ceremony where Minni Minawi is appointed governor of Darfur, in el-Fasher, Sudan - Wednesday 8 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane sun taru don ganin Minni Minawi zababben gwamnan yankin Darfur na Sudan ranar Laraba.
Lt-Gen Abdel Fattah Abdelrahman Burhan (L) next to newly inaugurated Darfur governor Minni Minawi in el-Fasher, Sudan - Wednesday 8 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lt-Gen Abdel Fattah Abdelrahman Burhan daga hagu, ya halarci bikin - yana riƙe da hannun Mr Minawi, wani tsohon ɗan tawaye...
Sudan Liberation Movement fighters at a ceremony where Minni Minawi is appointed governor of Darfur, in el-Fasher, Sudan - Wednesday 8 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mr Minawi ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a madadin ƙungiyar Sudan Liberation Movement (SLM) da sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya a bara. Wasu mayaƙan SLM ma sun halarci taron...
People up a tree at a ceremony where Minni Minawi is appointed governor of Darfur, in el-Fasher, Sudan - Wednesday 8 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sauran mutane sun hau kan bishiya don ganin sabon gwamnan...
A wildfire illuminates the night sky in Metline, Tunisia - Tuesday 10 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata gobarar daji na ci da daddare a kusa da gaɓar teku a arewacin Tunusiya a ranar Talata. Al'ummomi suna ta ƙoƙarin kashe gobarar wacce take shafar Aljeriya da ke maƙwabtaka...
Girls cool off in the Mediterranean sea waters at a beach off La Goulette, Tunisia - Tuesday 10 August 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yanayin zafi ya ta'azzara a biranen Tunusiya da ke kusa da Bahar Rum a ranar Talata.- inda mutane suka dinga zuwa gaɓar teku don sanyaya jikinsu.
Team Egypt compete in the Artistic Swimming Team Free Routine at the Tokyo Aquatics Centre in Tokyo, Japan - Saturday 7 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata ƴar Masar da ke ninƙaya tana shirin yadda za ta yi wasanta a Gasar Olympics a Tokyo a ranar Asabar…
Kenya's Peres Jepchirchir crossing the finish line at the women's Olympic marathon in Sapporo, Japan - Saturday 7 August 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wannan ranar wata ƴar Kenya Peres Jepchirchir tayi nasara a tseren mata a Gasar Olympic...
Kenya's Eliud Kipchoge crossing the finish line at the men's Olympic marathon in Sapporo, Japan - Sunday 8 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ɗan ƙasar shi ma Eliud Kipchoge ya yi nasara a gasar tseren maza a washe gari.
An elephant calf crosses a road in the Amboseli National Park, Kenya - Tuesday 10 August 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Talata wasu giwaye suna tsallaka titi a Gandun Daji na Amboseli na Kenya.
Libyan men feed pigeons in an empty Martyrs Square in downtown Tripoli, Libya - Saturday 7 August 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu ƴan Libiya na ciyar da tattabaru abinci a Dandalin SHuhada'u a tsakiyar babban birnin ƙasar tripoli, a ranar Asabar.
Members of Magic System being filmed in the Anoumabo neighbourhood of Abidjan, Ivory Coast - Sunday 8 August 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An ɗauki fim ɗin mambobin fitacciyar ƙungiyar mawaƙa ta Ivory Coast ta Magic System a birnin Abidjan ranar Lahadi...
A car wash attendant asleep on a chair with his head resting on a vehicle, Lusaka, Zambia - Tuesday 10 August 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai wankin mota na barci a Lusaka babban birnin Zambiya a ranar Talata - inda a can gefe kuma ga tarin latifu a cikin wata babbar mota.
The silhouettes of people queueing up to vote seen on a wall with the word "Vote" painted on it - Thursday 12 August 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwana biyu bayan nan mutane suka fita layin zaɓe a Lusaka.
Nigerian striker Kelechi Iheanacho holding the Community Shield at Wembly, the UK - Saturday 7 August 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dan ƙwallon Najeriya Kelechi Iheanacho na murna bayan da ƙungiyarsa ta Leicester City ta ci kambun Community Shield a Wembley ranar Asabar.
1px transparent line

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka