Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi Gusau

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi Gusau
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon:

Fitaccen malamin addinin Musulunci na Najeriya Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi ya ce ya kwadaitu da neman ilimi ne tun yana karamin yaro saboda da ma gidansu gida ne na malamai.

Ya bayyana haka ne a shirinmu na Ku San Malamanku.

Malamin ya bayyana cewa da yake gidansu gida ne da ke da tarihi mai tsawo na ilimi don haka ya tashi ya yi karatu a gaban mahaifinsa Sheik Muhammadu Sodangi wanda ya yi musu tarbiyya a kan neman ilimi da kuma yin aiki da shi gwargwadon hali.

Ya ce "don haka na yi karatun Alkur'ani mai girma a hannun mahaifinmu har na yi nisa cikinsa inda daga baya ya mika mu a hannun kawunmu Malam Aliyu Abdullahi ya ci gaba da karantar da mu har muka sauke Alkur'ani."

Malamin, wanda aka haifa ranar sha18 ga watan Agustar shekarar 1960 a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda kuma a nan ne ya tashi, ya ce yana da dangantaka da mujaddadi Usmanu.

''Akwai dangantaka ta jini da kakanmu na biyar da Sheik Usman Dan Fodio da malamansu da suka karantar da su, don haka kakan namu na daga cikin mukarraban Shehu Usman Dan Fodio,'' in ji malamin.

Fafutikar neman ilimi.

Bayan saukar karatun ne, in ji malamin, mahaifinsu ya dawo gida don zaman na din-din-din daga tafiye-tafiye zuwa garuruwa don karantarwa, sai ya ci gaba da karantar da su litattafan addinin musulunci.

Daga bisani kuma mahaifin nasu ya kai shi cikin makarantar da suke karatu na litattafai wato makarantar zaure inda malamai manyan dattawa ke karatu.

Ya yi karatu a makarantar malam Sulaiman Kofar Jangeme Yara da kuma makarantar malam Muhammadu Narke Sarki inda ya kasance mafi kankantar shekaru a makarantun a wancan lokacin.

A cewar malamin, "Ni kadai ne mai kananan shekaru cikin iyaye da kakanni, kuma na yi saurin haddace litatafai irin su risala, da su hadisai da sauransu saboda idan na dawo gida na kan rika maimaitawa.

"Sai mahaifina ya ce min ka ga shi ya sa na kai ka can cikin manyan malamai ka zauna ka rika karatu."

Bayan da Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi ya ci gaba da karatun ne a garin na Gusau kuma mahaifin nasa ya dauke su shi da wasu abokansa zuwa wata makaranta da ya yi karatu a garin Zaria jihar Kaduna inda wani shahararren malamin addinin musulunci Malam Muhammadu Inuwa yake karantarwa.

A garin na Zaria ne malamin ya ci gaba da karatu kuma daga bisani ya sake dawowa gida inda mahaifin na su ya kafa makaranta bayan da ya daina yawon karatun, kuma ya ci gaba da tsaron bangaren yara na makarantar a yayin da shi kuma yake bangaren masu karatun litattafai.

line

'Kundin Malamaina'

Malamin ya kuma bayyana cewa ya yi karatu a hannun malamai da dama wanda ya rubutu sunayensu duka a wani kundi ya yi wa lakabi da Malamai na.

"Cikin su akwai Malam Muhammadu Sodangi wato mahaifina, da 'yanuwanshi su malam Aliyu, da malam Abubakar Kwaire, da Faruk Abdullahi, sai malam Isa Shuwai limamin masallacin Tudun Wada, wanda na karanci tafsiri na nahawu a wajensa da kuma fannin kimiyyar taswiarar kasa wato Geography," in ji shi.

Malamin da kuma ce ya samu dimbin ilimi na Hadisai da Tafsiri da kuma luggar Larabci da Fiqihu, da Sarbu da ka'idojin rubuta ta tarbiyyar dalibi kan zamantakewa da sauransu dama a hannun sauran malaman.

Ya kuma kara da cewa yana da wasu malamai da bai zauna karatu a wajen sub a amma ya yi amfani da litattafansu da kasidunsu da fatawowainsu da sakonninsu dama wajen yada ilimi tun kafin bullowar shafukan sada zumunta.

"Mukan yi amfani da hanyoyi aikewa da wasiku wajen aikewa da kasidu ana aiko mana da litattafai zuwa kasashen Saudi Arabia, da Misra, sudan Libya Sudan da kuma Pakistan."

'Mahaifina na cikin masu kyamar ilimin Boko'

Duk da cewa mahaifin Sheik Abubakar Sodangi na cikin wadanda ke kyamar ilmin Boko amma ya bari dansa ya yi karatu sakamakon wasu dalilai.

"Mahaifina na cikin wadanda suke kyamar ilimin Boko wanda ba ya rasa nasaba da tun da su suke da Daular Usmaniyya kuma a gabansu aka yi yakin da aka kafa Daular lokacin kakana suna matasa sun san mutanen da suka yi shahada a wannan yakin.

"A gaban su Sarkin Musulmi Attahiru ya bar Sakkwato da ayari ana kuka ya tafi da tutar Musulunci ya ce ya yi hijira," in ji malamin.

"A gabansu Bature ya shigo ya tara al'ummar da suka rage wadanda suka ce ba zai yiwu a watse a bar Turawa a gari su mayar da mutane kafirai ba, a gaban su duk aka yi."

A cewar malamin, "Ka ga shi ya sa ga suka yi wa 'ya'yansu tarbiyyar kyamar Bature, don haka duk abin da zai hada su da Bature ba sa son shi."

Amma kuma, kamar yadda malamin ya bayyana, dalilan da suka sa ya samu ilimin bokon daga baya cewa a lokacin da kawunsa ya aurar da babbar yayarsu ga wani dan Boko ba tare da mahaifinsa ya sani ba, kuma ita ta dauke shi riko inda daga nan ne ya fara karatu.

"Daga baya da aka sanar da shi ina karatun Boko sai ya ce a dawo da ni bai yarda na yi boko ba, amma kuma daga baya aka fahimtar da shi cewa sai an hada da ilimin zamani za a samu cimma nasarar taimakawa da kuma yada addinin musulunci cikin sauki," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Gaskiya daga baya kuma mahifinmu ya ga amfanin abin, wanda shi ya sa na kara fadada karatuna na bokon."

line

'Nikaya da langa'

Da muka tambaye shi game da irin wasannin da ya yi lokacin yana matashi, Sheik Abubakar Sodangi ya ce buga kwallon kafa da langa da makamantansu sai dai "yanzu babu wasan da nake kewa kamar na iyo [ninkaya]".

Game da abinci, malamin ya ce yana sha'awar cin tuwo da miya musamman da daddare "amma na fi son wake da shinkafa da fura da nono."

Sheik Abubakar Sodangi ya ce yana da mata biyu da 'ya'ya maza da mata.