Jacob Zuma: An kwantar da tsohon shugaban Afirka Ta Kudu a asibiti wajen gidan yari

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An kwantar da tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma a wani asibiti da ke wajen gidan yari domin duba lafiyarsa, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.

Gidauniyarsa ta ce "ana duba lafiyarsa ne kamar yadda ya saba duk shekara" kuma babu buƙatar tayar da hankali.

A matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa ana duba lafiyar Zuma ne a sibitin soji, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Tsohon shugaban ƙasar na zaman gidan yari ne na ɗaurin wata 15 da aka yanke masa tun a ranar 7 ga Yuli.

Hukumomin gidan yarin sun ce yana da ƴancin neman magani kamar sauran ƴan gidan yarin da ake tsare da su.

Ma'aikatar shari'a ta wallafa sanarwar kwantar da tsohon shugaban a shafin Twitter inda ta ce an kwantar da shi ne a ranar Juma'a.

A mako mai zuwa, tsohon shugaban ake sa ran zai sake gurfana gaban kotu kan wani zargi na daban da ake masa da ya shafi cinikin makamai da rashawa.

Ya musanta zargin da ake masa da ya shafi kuɗi dala biliyan biyar.

Daurin da aka yi masa ya haddasa tarzoma a kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 300.