Ficewar dakarun kasashen waje daga Afghanistan ta sa an tuna da lamarin 1989

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Lyse Doucet
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief international correspondemt, Astana
- An wallafa
A lokacin da ake tsananin sanyi a birnin Kabul, ana kuma tsaka da yaki, an kawo min takardar gargadi ta karshe. "Dole na ba ki shawarar lallai ki gaggauta ficewa daga Afghanistan, har yanzu akwai jiragen fasinja da ke tashi," shawarar da ofishin jakadancin Birtaniya ya aiko min kenan.
Kwanaki 11 bayan nan, a ranar 30 ga watan Janairun 1989, ana tsananin sanyi da kuma zubar dusar kankara, muka ga yadda ofishin difilomasiyyar Amurka ya yi kwarya-kwaryar bikin ficewa daga kasar.
Makwanni kadan bayan haka kuma kashin karshe na sojojin Sabiya suka fice, abin da ya kawo karshen gwamman shekarun da suka kwashe suna aiki a Afghanistan. Ita ma Birtaniya ta rufe kyakkyawan ofishin da a wancan lokacin ake yi wa lakabi da wanda ya fi kowanne kyawu a yankin Asiya.
"Ministocin Birtaniya ba su da wani zabi face a rufe ofishin, duk da cewa yawancin ma'aikata na son ci gaba da zama domin gudanar da aiki," a cewar Stephen Evans, tsohon jakadan Birtaniya a Afghanistan.
Amurka da Birtaniya sun yi alkawarin sake komawa kasar nan ba da jimawa ba, amma za su rufe ofisoshin difilomasiyyarsu har sai dakarun da Amurka ke jagoranta sun murkushe mayakan Taliban a shekarar 2001.
Kusan shekaru 20 kenan, da dakarun kawancen Nato suka kawo karshen aiki tare da ficewarsu daga kasar, abin tambaya shi ne: shin su waye za su ci gaba da zama a kasar kuma su waye za su fice? Wannan shi ne batun da aka fi tattaunawa a kowanne lokaci a Afghanistan.

"Hakikanin gaskiya ba ma son bayar da wannan umarnin a halin da ake ciki wato rufe ofisoshin jakadancinmu, sai dai idan ana fuskantar matsalar tsaro," kamar yadda Mista Evans ya fada, a daidai lokacin da ake jin karar fashewar abubuwa ta bayan katangar da aka kewaye ta da waya mai kaifi.
Sai dai cikin takaitaccen lokaci kuma cikin gaggawa Amurka ta janye dakarunta, ga kuma sake tasowar mayakan Taliban, sai kuma uwa uba yadda ake samun karuwar yaduwar sabon nau'in cutar korona, duka sun taru sun sanya kasar cikin halin rashin tabbas.
Ana ci gaba da yi wa ma'aikata bayani akai-akai kan batun kwashe su zuwa gida, sai dai lamarin na dan tafiyar hawainiya saboda batun cutar korona da sha'anin tsaro, an kuma tattara wasu kaya a jakunkuna na ko-ta-kwana. An dan samu kwanaki cikin kwanciyar hankali, amma cike da taka-tsantsan.
"Duk abin da muka damu da shi da mayar da hankali akai shi ne batun tsaro," in ji wani jami'in difilomasiyya. "Watannin da suka gabata muna ta tattaunawa kan sha'anin tsaro a birnin Kabul, saboda mun zuba jari a nan, kuma muna son ci gaba da zama."
Ma'aikatan karshe na ofishin jakadancin Belgium sun fice a wannan makon, yayin da na Australia suka fice tun a watan Mayu. A iya cewa ma'aikatan Faransa sun kwashe nasu dakarun, sai dai Birtaniya na duba cikin tsanaki.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu da ke ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki su ne 'yan kasar Afghanistan, ciki har da masu yin tafinta, da ke taimakawa da fassarar yaruka tsakanin mutane da sojoji, da yawancin 'yan kasar da ke cikin tsoro da firgici wadanda albarkacin dakarun kasashen waje suke samun wutar lantarki, da samun kwanciyar hankali, sun kuma zuba ido a ofisoshin difilomasiyyar don ganin abin da ka je ya zo.
"Idan tuntuni an shaida wa kasar cewa za ta fuskanci gazawa irin wannan, shin wane kyakkyawan fata kake ganin 'yan kasar za su samu? Wannan ita ce tambayar da Muqaddesa Yourish, tsohon ministan kasuwanci Afghanistan, wanda ke jagorantar kamfanin sadarwa a birnin Kabul.
Sai dai 'yan Afghanistan sun fusata lokacin da gwamnatin Australia ta sanar da rufe ofishinta na Kabul a watan Mayu, duk da cewa matakin na wucin gadi ne. A wannan karon, ofishin jakadancin Birtaniya ba wasika ya aike ba, sako aka wallafa ashafin Tuwita, tare da bukatar 'yan kasar su "gaggauta ficewa daga Afghanistan".
"Abin damuwar shi ne mataki ne na kasashen waje, da alama duniya na jin nauyi kan janyewar da ka iya sake jefa kasar cikin mummunan yanayi fiye da a baya ko ma yakin basasa," in ji Mista Yourish. 'Yan Afghanistan ma na cike da fargaba kan barazanar yakin da ake ci gaba da fuskanta.
Duk da haka Birtaniya na sanya ido kan ficewar Amurka, haka ma sauran kasashe. Amurka ta ce tana shirin barin daruruwan dakarun da za su kula da ofishin jakadancinta, kamar dai yadda take yi a wasu kasashe.
Sai dai hakan ma ana yi cike da hadari. A makon nan, mai magana da yawun kungiyar Taliban, ya shaida wa BBC cewa za su kalli hakan a matsayin mamayar sojoji. Kuma Taliban ta kafe kan cewa tattaunawa da suka yi tsakaninsu ce ta share hanyar ficewarsu daga kasar.
"A lokacin tattaunawa da Amurka, duk wadannan batutuwan an tattauna a kansu, kuma bangaren Amurka sun amince su janye daga dakarunsu, da masu ba su shawara da masu ba da horo daga Afghanistan," in ji mai magana da yawun Taliban Suhail Shaheen a lokacin da na tambaye shi kan wannan batu.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Taliban da take son ganin kasashen waje sun amince da sahihancinta, ta zuba ido sosai kan ofisoshin difilomasiyyar kasashen.
A watan da ya gabata, Tomas Niklasson, sabon jakada na musamman na tarayyar turai a Afghanistan, ya nuna damuwa kan sha'anin tsaro a taron da suka yi a birnin Doha da shugabannin Taliban, sun fitar da sanarwa sa'o'i kadan bayan taron, kan cewa za su bai wa duk jami'an difilomasiyya da na jinkai kariya.
Sai dai ba kowa ne ya aminta da hakan ba.
Yayin da Taliban ke son wakilan kasashen waje su ci gaba da kasancewa a Kabul, a bangare guda kuma ba sa son su yi aikin da suka saba, wato bai wa gwamnati goyon baya.
A yanzu yawancin ofisoshin da suke yankunan da suke da matukar tsaro da ke waje-waje na son sake nausawa ciki domin samun karin tsaro. Norway ta amince ta ci gaba da aiki a asibitin da aka kafa domin jami'an difilomasiyya da ma'aikatan agaji har zuwa lokacin bazara mai zuwa, wanda kafin lokacin ana sa ran an kammala gina asibitin farar hula.
Wani abu mai matukar muhimmaci ga 'yan Afghanistan shi ne filin jirgin sama, wanda idan lamura suka rincabe shi zai zama hanyar da za a kwashe mutane.
A yanzu dakarun kasar Turkiyya da Amurka ne ke gadin filin jirgin sama na Hamid Karzai, karkashin jagorancin dakarun tsaron NATO. Ana fatan dakarun Turkiyya za su ci gaba da kasancewa a nan, karkashin wata yarjejeniya da suka kulla da Afghanistan.
Sai dai har yanzu ana tattaunawa mai tsauri da gwamnatin Turkiyya kan batun siyasa, tsaro, da shari'a, baya ga taurin kan mayakan Taliban. Sai dai jami'an NATO na da kwarin gwiwar za a iya cimma matsaya.

Asalin hoton, Getty Images
Don haka yawancin ofisoshin jakadancin kasashe ba su nuna alamun za su ci gaba da kasancewa a kasar ba.
"Ofishin jakadancin Amurka a Kabul yana bude, kuma zai ci gaba da kasancewa a bude," kamar yadda ofishin ya wallafa a shafinsa na Tuwita, a lokacin da kafafen yada labarai suka fara rawaito cewa akwai yiwuwar kwashe ma'aikatan ofishin zuwa gida.
"Ofisoshin difilomasiyya za su ci gaba da kasancewa a bude a birnin Kabul," in ji wani jami'in difilomasiyya. "Sai dai muna cikin wani lokaci mai wuya da tsauri, za mu sa ido don ganin halin da ake ciki. Bai wa ma'aikatanmu kariya shi ne abu mai muhimmanci a gare mu."
"Ofishin difilomasiyyar Birtaniya zai sa iso kwarai," kamar yadda wani jami'in ya bayyana a Kabul. "Ba wai ayyukan kasashen yammacin duniya ne kadai ba. Hatta jakadan China ya bayyana aniyar tattaunawa kan karin jami'an tsaro."
Farfajiyar ofishin jakadancin Birtaniya da ke yanki mai matukar tsaro ta fi girman wani ofishin, amma tana da kusanci sosai da sauran, don haka ake mata kallon ja gaba.
A yanzu dukkan 'yan Afghanistan da kasashen waje sun zuba ido domin ganin yadda za a yi musayar tsaro cikin gaggawa a cikin kasar.
"Ba a damu da yawancin gundumomin da mayakan Taliban suka karbe iko da su ba, sai dai suna da amfani ta fuskar yada farfaganda," kamar yadda tsohon mataimakin ministan tsaron Afghanistan Tamim Asey ya yi nazari, wanda a yanzu shi ne ke jagorantar cibiyar yaki da tabbatar da zaman lafiya a Kabul. "Kakar yaki da za a fuskanta nan gaba, ita ce yaki tsakanin birane."











