Makomar Afghanistan: Makarantar matan da aka buɗe cikin sirri don gudun harin 'yan Taliban

- Marubuci, Daga Zuhal Ahad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Dari
- An wallafa
Yayin da dakarun Amurka da na kungiyar tsaro ta NATO ke ci gaba da janyewa daga kasar Afghanistan, BBC ta tattauna da wasu mata uku masu zamani daban-daban game da fargabar da suke da ita kan makomarsu.
Wata gogaggiyar malamar makaranta, da wata dalibar da ta kammala karatun jami'a, da kuma wata dalibar, duka sun bayyana yadda a lokacin annobar korona suka rika fama da matsalar rashin samun damar amfani da fasahar zamani da nuna wariyar jinsi, da kuma a'ladar tashin hankali.
Ba wannan ne karon farko da Shahla Fareed ta fara boye litattafanta ba, kuma ba shi ne karon farko da ta fara tsara yadda za ta je makaranta a asirce ba.
Damar samun ilimi ga 'ya'yan Shahla da ma sauran mata a fadin kasar ta Afghanistan ta sake fadawa cikin barazana.
Malamar makaranta
Shahla malamar makaranta ce a Jami'ar Kabul babban birnin kasar.
Lokacin kullen korona ta ci gaba da koyar da darussa, amma ta ce dalibanta da dama na fama da matsalar samun shiga shafin intanet.
"Akasarin dalibai mata ba su da wayoyin salula, haka ma iyayensu ba sa amincewa su yi amfani da shafin intanet.
Wadanda kuma ke amfani da wayoyin salular 'yan uwansu maza sukan sa ido a kansu lokacin daukar darasi don ganin wadanda suke magana da su," in ji ta.
Amma ba wai batun rashin 'yancin amfani da fasahar zamani ne kadai ke yi wa matan cikas ba.
Rikicin da ke ci gaba da faruwa a tsakanin gwamnati da dakarun kungiyar Taliban yanzu ya kai makura.
Yayin da ake ci gaba da shaida janyewar dakarun da Amurka ke jagoranta, mutane da dama suna fargabar sabbin hare-hare na kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama.
A cikin watanni kadan da suka gabata ne kungiyar ta Taliban ta yi ikirarin samun galabar karbe ikon wasu yankuna.
A kokarinta na kafa gwamnatin da maza ke mamayewa, kungiyar Taliban ta haramta wa mata samun ilimi, da kuma hana matan yin aiki ko kuma fita daga gidajensu ba tare da muharramansu ba.

Tuni da ma kungiyar masu rike makaman take adawa da ilimin 'ya'ya mata.
Yayin da yake magana da BBC a madadin kungiyar Taliban, Zabihullah Mujahid ya ce: "Ya kamata duka maza da mata su samu 'yancin ilimi kuma yana da matukar muhimmanci. Amma ya kamata a samar da wuri na musamman ga matan, kuma ya kamata a samar da malamai mata."
Amma kuma, kungiyoyin kare hakkin mata da ma mata da dama da suka hada da Shahla na ganin akwai babbar fargaba, da alama za a sake hana ilimin 'yaya mata gaba daya.
Yanzu a shekaru 60, Shahla ta bayyana yadda ta bude makarantar 'yan mata a asirce a shekarar 1970 lokacin da kungiyar Taliban ta karbe daukacin ikon kasar.
Dalibanta da dama daga shekaru tara zuwa 10 kan zo sanye da hijabi fuska a rufe ko kuma burka mai launin shudi. A koda yaushe takan fada musu su rika boye litattafan turancinsu a cikin sauran litattafan addinin Islama don gudun kada a kama su.
Zaune a cikin lambu da ke bayan gidanta a karkashin wata bishiya da kuma rumfar yadi, Shahla kan koyar da daliban ta hanyar amfani da wani karamin bakin allo.
"Na fara gudanar da makarantar da dalibai mata 20 amma na karasa da guda hudu kacal. Biyu daga cikinsu 'yayana ne" in ji Shahla, tana bayyana yadda yake da matukar wahala wajen ganin daliban sun dore wa karatun.
Ta ce kungiyar Taliban tana yawan kai sumame gidan don gano duk wata shaida game da makarantar, amma sau daya ta rufe makarantar shi ma "na wucin gadi" ne.
Yanzu bayan shekara hamsin, Shahla ta ce ta shiga damuwar cewa dole ta sake neman litattafai ko da za a sake bude makarantar.
Daliba
Wahida, mai shekaru 16, tana zaune a garin da tafiyar sa'oi bakwai a mota ce take kai mutum, daga gidan Shahla.
A ko wace rana cikin mako Wahida kan taka zuwa makaranta ita da kanenta. Amma fatan da take da shi na zuwa makaranta na matukar bata wa iyayenta rai.
Mahaifinta da kakarta sun daina yi mata magana baki daya.
"Sun ce dole in bar makaranta kuma in yi aure," in ji ta.

Wahida na zaune tare da danginta a lardin Kandahar, inda kungiyar Taliban ta samo asali kuma inda akasarin gundumomi ke karkashin ikonta.
A cikin duka gundumomi 17 a lardin, guda uku kacal ne ke da makarantar 'yan mata.
BBC ta tambayi shin me ya sa gundumomi da dama ba su da gurbi na samar da ilimin 'ya'ya mata.
Zabihullah Mujahid, wani jami'in kungiyar Taliban ya ce: "A lardunan Kandahar da Helmand an rufe makarantu saboda fada ya kazanta. Ko makarantun maza ma kadan ne.
"Kuma wannan wani tunani ne irin na mutane, bayan yanayin al'adu da zamantakewa na nufin mutane kadan ne ke tura 'ya'yansu mata makaranta. Yana bukatar lokaci kadan, amma daga bangarenmu babu wata matsala.''
Wahida ta ce da taimakon yayanta da mahaifiyarta ne ta samu damar yin karatu.
Mahaifiyarta, wacce ba a taba bari ta shiga makaranta ba, ta fada wa diyarta cewa dole ta yi fafutukar neman 'yancin mata duk kuwa da kara bazuwar rikicin.
"Ina fata zan iya saka burin mahaifiyata ya zama gaskiya. Amma a halin da ake ciki na damu matuka cewa ba zan iya kammala karatuna ba, ballantana zuwa jami'a na zama mai fafutika ga saura."
Amma Wahida na cike da fata, saboda labarai irin na Shamsia Alizada.
Dalibar da ta kammala karatu a jami'a
Akwai wasu 'yan mata wadanda ba su samu 'yancin amfani da fasahar zamani ba, saboda rikicin da ke faruwa, da nuna wariyar jinsi da kuma annobar korona, suna ci gaba kokarin kasancewa masu zama abin koyi.
A shekarar da ta wuce Shamsia ta samu maki mafi girma fiye da duka dalibai 170,000 da suka zauna jarrabawar shiga jami'ar.
A matsayinta na diyar mai hakar ma'adanin kwal, ta girma a daya daga cikin yankunan birnin Kabul mai fuskantar barazana, da akasari ba su samu damar da ta kamata ba.
A shekarar 2018, kungiyar IS ta kai hari makarantarsu. Dalibai 'yan uwanta fiye da 46 ne suka halaka.

Kana a shekarar 2020, bayan da suka koma wata unguwa da ke kusa, kungiyar IS din ta sake kai hari kan sabuwar makarantar da ta koma.
"Karatu a Afghanistan akwai matukar wahala kuma ina jin tsoro sosai. Amma cibiyar iliminmu ta dauki gagarumin mataki wanda ya taimaka min na samu kwanciyar hankali. Kuma idan kana cikin karatu, ba ka da lokacin tunanin wani abu game da tsaro,'' in ji Shamsia.
Bayan da ta samu nasarar tallafin karatu zuwa kasar Turkiyya, yanzu Shamsia tana samun horon zama likita.
Kungiyar ISIS - sabuwar barazana
A watan Nuwambar da ya gabata, Shahla na koyarwa a Jami'ar Kabul lokacin da 'yan bindiga da dama suka kai farmaki harabar makarantar suka bude wuta a wani aji da ke kusa da ita.
"Ina wajen bikin baje-kolin litattafai lokacin da na ji wata kara da kuma harbe-harbe. Dalibai na ta guje-guje ta ko ina, wasu na ta kuka kana saura amsa wayoyi suna ta gudu zuwa babbar kofar fita," in ji Shahla. "Bayan da dakarun tsaro na gwamnati suka iso, fada ya rincabe tsakanin bangarorin biyu kuma sun shafe sa'oi."
Mutane 22 ne suka rasa rayukansu kuma fiye da 22 suka samu raunuka.
"Akasarin wadanda harin ya rutsa da su 'yan mata ne," in ji Shahla. "Kuma ko jami'an 'yan sanda ba su yarda su taimaki matan da suka samu raunuka ba su tsere saboda imanin da suka yi cewa taba mata haramun ne [a bisa dokar Musulunci ]."
"Amma daga bisani lokacin da dakaru na musamman suka iso ne, suka kwashe 'yan matan.''
Daga bisani kungiyar ISIS ta fito ta yi ikirarin kai harin, tana mai cewa sun kai harin ne saboda masu kammala karatu a fannin shari'a da masu bincike da ta ce ke aiki wa gwamnati Afghanistan mai ridda."
Kungiyar ISIS-K, wani bangare na kungiyar masu jihadin, an kafa ta ne a kasar ta Afghanistan a shekarar 2014.
Tun bayan nan, sun yi ikirarin daukar alhakin kai munanan hare-hare a kan babban birnin da suka hada da makarantu da cibiyoyin ilimi.
Mata da kananan yara, da suka hada da jarirai na cikin wadanda munanan hare-haren da kungiyar ISIS ta yi ikirarin kaddamarwa a shekarar da ta gabata.
Wani hari da aka kai a sashen haihuwa na wani asibiti ya haddasa mutuwar mutane 16 da kuma jikkata fiye da 16.

Ita kuwa Shahla, wacce ta jajirce kan batun samar da ilimi, cewa take wannan rikici na kungiyoyin masu tayar da kayar baya kamar su ISIS da ke kara bazuwa da kuma fadada a yankunan kungiyar Taliban ne ya sa dole ta sake bukatar hada litattafai.
"Dole in tabbatar da cewa ina da isassun kudi na kafa rumfa, da litattafan karatu, da na rubutu da alkaluman rubutun. Saboda na san kungiyar Taliban ba za ta taba amincewa 'yan mata su yi karatu a makaranta ba, ko a yanzu ma lokacin da suka karbe ikon wata gunduma, abu na farko da suka fara yi shi ne rufe makarantun 'yan mata," in ji ta.
Jilla Dastmalchi ce ta yi zane-zanen hotuna











