Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu: Kotun hukunta mazajen da suka bar matansu tsawon lokaci a Nijar

Bayanan sautiCi-rani a Nijar: Kotun hukunta ma'auratan da suka aikata baɗala
An wallafa

Latsa hoton sama ku saurari cikakken shirin

A cikin shirinmu na musamman kan ci-ranin mutanen Tahoua na jamhuriyyar Nijar, AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya ziyarci kotun da ke yin sasanci da hukunta mazajen da suka yi lalata da matan aure.

Yawan tafiye-tafiyen don neman kuɗi kan sa maza su bar matansu tsawon lokaci, abin da ke jawo wasu su yi amfani da wannan damar domin aikata kwartanci.

Shirin na zuwa muku ne a madadin filin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu.