UN: Farashin abinci na ƙaruwa cikin sauri a shekara 10

An wallafa

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce farashin abinci a duniya ya tashi cikin sauri a wata guda sama da ko wanne wata a shekara 10.

MDD ta yi amfani da alkaluman hauhawar farashi na duniya, wanda ya yi tashin gwauron zabi sama da wata 12 a jere.

Masu kawo abinci sun rika fuskantar koma baya saboda yankewar sarrafa abinci da safarar shi da kuma aiki a kanshi lokacin annobar korona.

Damuwa na karuwa kan hauhawar farashi da kuma karuwar kuɗin cefane wanda ya yi tasiri kan tattalin arzikin duniya.

Shirin samar da abinci na MDD ya bibiyi alkaluman farashin abinci a fadin duniya, wadanda suka hadar da nama, sikari da abincin da aka sarrafa daga hatsi da mai da dai sauransu.

A wannan shekara farashin na karuwa da 39.7 a watan Mayu - tashin farashin wata guda da ba a bata gani ba tun watan Oktoba 2010, kamar yadda alkaluman suka bayyana.

Duka bangarorin biyar din da suka janyo tashin alkaluman, sunzo ne biyo bayan tashin farashin kayan miya da mai da sukari da kuma kwayoyi kamar su (gero da dawa).

Wannan ya harba farashin kayan sama a dukkan mataki wanda tun Satumbar 2011 rabon da a ga haka.

Karin da aka samu na zuwa ne sakamakon bukatar da wasu kasashe ga kuma karacin samar da kayayyakin da ake fama da shi.

Kasuwanci da kuma yadda ake safarar abincin ya samu katsewa saboda takaita zirga-zirga da aka yi, hakan kuma ya janyo yankewar abinci da tashin farashinsa.

Kwararu sun yi gargadin cewa yawan bukata da kuma karancin samar da abinci zai iya janyo karuwar farashin abinci lokacin da aka sanya dokar hana fita.

Amma da alamun wasu kamfanonin za su iya samun habbaka. Shirin samar da abinci na MDD zai samar da hatsi da dangoginsa a wannan shekarar, wanda ake sa ran hakan zai rage damuwa da ake da ita.

Mene ne hauhawar farashi?

Karuwar farashin kayayyakin amfani na rayuwa da ake samu shi ke kira hauhawar farashi.

Haka kuma kari akan farashin yadda yadda muke siyan kaya a manyan kantina da yadda muke biyan kudade idan an mana aiki, har da kudaden ruwan da ake kara mana.

Daya daga cikin manyan matakan da suke karawa bangaren kudi tagomashi, saboda yakan shafar masu saya da kudadensu.