Ku san Malamanku tare da Sheikh Muhammad Kabir Umar
An haifi Sheikh Muhammad Kabir Umar a garin Maradun na jihar Zamfara a shekara ta 1966.
Duk da mahaifinsa malami ne na Islama, bai kasance mai ƙyamar boko ba don haka an sa Sheikh makarantar boko kuma ya kammala a 1977.
Daga nan ne kuma ya wuce Sheik Gumi College a jihar Sokoto kuma ya kammala a 1982.
Sheikh ya ce bayan nan ne ya tafi Makarantar Horar da Malamai da ke Okene a jihar Kogi inda ya kammala da NCE a 1985.
Daga nan ne ya koma gida Zamfara inda ya ci gaba da koyarwa a zamanin jihar na cikin jihar Sokoto kuma ya koyar a makarantun sakandire da dama.
Cikin shekarun 1990 sai ya koma Jami'ar Bayero da ke Kano don samun digirinsa na farko amma bai kammala ba sai ya samu shiga jami'ar Islamiyya ta Madina a Saudiyya.
Ya dawo daga Madina a shekarar 2002 bayan kammala karatunsa inda daga nan sai ya soma koyarwa a Makarantar Horar da Malamai da ke Maru a jihar Sokoto.
Daga baya ya koma Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto inda ya yi digirinsa na biyu. A halin yanzu yana fatan yin digirinsa na uku inda zai rubuta littafi kan Shehu Usman Ɗanfodiyo.

Me Malam ya fi alfahari da shi?
Sheikh Muhammad Kabir Umar ya ce cikin abubuwan da ya ke alfahari da su ciki har da zuwansa Jami'ar Madina saboda gwagwarmayar da ya sha kafin ya samu shiga jami'ar.
Ya ce an kai matakin da har ya fitar da rai da shiga jami'ar shi ya sa ma ya koma Jami'ar Bayero ta Kano don yin digiri kuma yana cikin yi ne ya samu tafiya Madina.
Wani bincike da ya yi game da littafin Bulugul Maram ne ya taimaka masa wajen shiga Jami'ar ta Madina inda malamai suka jinjina wa ƙoƙarin da ya yi wajen yin binciken.
Waɗanne ƙalubale Malam ya fuskanta?
Ya ce rayuwa gaba ɗaya ƙalubale ce, amma yana fuskantar ƙalubale a wajen karatu inda ya ce yana ganin kamar har yanzu bai yi komai ba.
Ya ce akwai ƙalubale yanzu na bincike dangane da karatun yanzu na zamani.
"A halin da ake ciki yanzu dole duk wani malami da ɗalibi ya zama cikin bincike saboda ya zama yana biye da abubuwa yadda ko yaushe zai zama a ilimance yake magana," in shi.
Ya ƙara da cewa: "Musamman tun da yanzu duk abin da ka faɗi a matsayinka na malami akwai hanyoyin tabbatar da su."
Waɗanne malamai ne suka fi tasiri a rayuwarsa?
Ya ce malamansa na Madina duk sun yi tasiri a rayuwarsa.
Amma a gida Najeriya akwai Malam AbdulWahab Kano wanda ya zama babban malaminsa da Sheikh Jafar Mahmud Adam wanda shi ma Sheikh Muhammad Kabir ya yi karatu a hannunsa.
Sanna akwai Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo shi ma ya yi karatu a hannunsa musamman karatun Hadisai na Bukhari da Muslim da Abu Dawood.
Haka kuma, Farfesa Mansur Sokoto ma ya yi tasiri a rayuwar malamin.
Abincin da Malam ya fi so
Malam ya ce abin da ya fi son ci shi ne nama, amma yanzu saboda shekarunsa sun fara ja ya rage cin naman don samun cikakkiyar lafiya.
Amma yana cin naman kaza har yanzu.
Haka kuma malam ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da ke ba shi nishaɗi shi ne tafiya da ƙafarsa.
"Ko aikin hajji da umra na je da ƙafa na ke zuwa ko ina," a cewar Sheikh Muhammad Kabir.












