Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Yakubu Musa

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Malam Yakubu Musa
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Malam Yakubu Musa, shi ne shugaba na farko na majalisar Shari'ar Musulunci a Najeriya mai suna Supreme Council for Shari'a in Nigeria kuma masanin Shari'a wanda ya yi karatu a wurare daban-daban.

Malamin wanda ɗan ɗariƙar Tijjaniyya ne a baya, shi ne shugaban ƙungiyar Izala na Jihar Katsina ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

An haifi Yakubu Musa a garin Gagaryaga da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gwaram - ta Jihar Jigawa a yanzu - ranar 1 ga watan Janairun 1950.

Ya yi karatun Alƙur'ani a garuruwan Kano da Jigawa da Katsina da Jos. Yanzu mazaunin Katsina ne, inda ya shafe kusan shekara 40 a garin.