Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rahoton kwamitin El-Rufa'i na so a cire tallafin mai a Najeriya
Wani kwamiti da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya jagoranta ya bayar da shawarar gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur.
Malam El-Rufa'i ya gabatar da wannan shawara ce a yayin taron ƙungiyar gwmanoni a ranar Laraba da daddare, wanda aka yi shi ta intanet.
Sai dai, ba kamar yadda aka ruwaito da farko cewar gwamnonin suna so a mayar da farashin man fetur naira 385 duk lita daya bisa ga shawarar rahoton na El-Rufa'i ba, NGF ta musanta haka.
AbdulRazaq Bello Barkindo, shugaban yada labarai da harkokin sadarwa na ƙungiyar ya ce maganar ba haka ta ke ba, "Shi El-Rufa'i ya gabatar da rahotonsa ne shi ne aka tattauna don a ji ra'ayin kowa amma ba a kai ga yanke hukunci ba."
"Ba za a kai ga yanke hukunci ba har sai an tattauna a taron NEC da matamaikin shugaban ƙasa ke jagoranta sannan za a san matakin da za a yanke a kan shawarar rahoton El-Rufa'in," a cewarsa.
Ya ce a lokacin da ake tattaunawar har aka zo kan gaɓar wannan batun wasu gwamnonin sun fita daga taron. Don haka ba sa nan aka gabatar da rahoton na El-Rufa'i.
Barkindo ya ce ainihin kwamitin El-Rufa'in ya yi bincike nan kan tsadar man fetur a Najeriya da wasu ƙasashen musamman maƙwabtanta.
"Shi El-Rufa'i yana ganin idan aka ci gaba da sayar da mai kan Naira 165 masu ɗauka a tirela su kai wasu ƙasashen za su riƙa samun ƙazamar riba ta wasu miliyoyi, wanda hakan zai sa fasa ƙwaurin man ya sake ƙamari."
"A ganinsa, maganin hakan shi ne a ƙara kuɗin mai ta yadda ƴan fasa ƙwauri ba za su iya ci gaba da fitar da shi ba, idan ba haka ba, ba za a shawo kan matsalar ba," a cewar Barkindo.
Barkindo dai ya ce ba shi da masaniya ko za a cimma matsaya a taron NEC na ranar Alhamis kan ƙarin farashin man amma dai ya san za a yi muhawara kan batun tsakanin gwamnoni da mataimakin shugaban ƙasa.
Rahotanni sun ce a yayin gabatar da rahoton a wajen taron, Gwamna El-Rufa'i ya bayyana cewa duk wata gwamnati na kashe tsakanin naira biliyan 70 zuwa biliyan 210 kan tallafin man fetur, wanda ake sayar da litarsa a yanzu kan naira 162.
Sannan kuma kwamitin rabon arzikin kasa na gwamnatin tarayya FAAC, zai samu tsakanin tiriliyan 1.3 da tiriliyan 2.2 duk shekara.
Wasu labaran masu alaka
Kazalika kwamitin gwamnan ya bayar da shawarar cewa gwamnatin tarayya ta sayar da matatun man kasar uku bayan an gyara su.
Sai dai akwai wasu gwamnoni da suka soki shawarwarin da cewa hakan sai kara jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali, kuma zai yi wahala kungiyar kwadago da 'yan kasar su yarda.
Sai dai mafi yawan gwamnpnin kuma na ganin gara a janye tallafin man fetur din tun yanzu maimakon a yi ta bata lokaci bayan kuwa an san cewa hakan na da matukar muhimmanci.
Kwamitin ya bayyana jihohin Legas da Oyo da Ogun da Rivers da kuma Abuja a matsayin wadanda suka fi amfani da man fetur.
Ba wannan ne karon farko da aka fara yunkurin janye tallafin man fetur ba a Najeriya. Sai dai a duk lokutan da batun ya taso kungiyoyin kwadago da kuma al'ummar kasar na bujire wa hakan.
Sauran batutuwan da gwamnonin suka cimma
Wannan shi ne karo na bakwai da gwamnonin kasar suka gudanar da taronsu a bana, inda suka tattauna kan batutuwa da dama, kamar yadda AbdulRazaq Bello Barkindo, shugaban tafiyar da harkokin yada labarai da sadarwa na kungiyar gwamnonin Najeriya, ya shaida wa BBC.
Batutuwan da suka tattauna sun hada da:
1. Batun yajin aikin da ma'aikatan shari'a na kasar ke yi, kan neman a ba su damar cin gashin kansu ta fuskar kason kudadensu daga asusun tarayya.
A yanzu dai gwamnonin sun amince da bukatun ma'aikatan shari'ar, amma sun ce sai ma'aikatan sun koma bakin aiki, don a yi tsarin da ya kamata kan lamarin.
2. Kididdigar manoma a Najeriya baki daya, don a san kowane manomi a ina yake da gona, wane irin albarkatun gona yake sarrafawa.