Yadda za ku gane idan azumin da kuka yi na Ramadan ya karbu
Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron cikakkiyar hirar Sheikh Triumph
Limamin masallacin Triump, Sheikh Lawal Abubakar Shu'aib ya ce magabata sun ce dorewar ayyukan alherin da mai azumi ya lakanta a watan Ramadan na nuna irin yadda mutumin ya yi dace a watan.
Ya ce "ba karamar hasara ba ce ga mutum a ce bayan watan Ramadan bai iya ci gaba da abubuwan da ya koya ba na ayyukan alheri kasancewar watan ramadan makaranta ce."
Sheikh Lawal ya kara da cewa magabata na cewa dorewa da ayyukan alheri bayan Ramadan na nuna mutum ya ci jarrabawa a watan Ramadan a saboda haka ya kamata musulmi ya ci gaba da ibada kamar sallar dare da karatun alkur'ani da yawan ciyarwa da kuma kyauta.
Dangane da sallar dare, Sheikh ya ce "ba wai ana nufin mutum ya takuarawa kansa ba. Abin da ake nufi shi ne mutum ya kasance yana sallar dare daidai gwargwado.
Abin da ake so shi ne mutum ya dawwama yana aikin alkairi duk kankantarsa."
Har wa yau, Sheikh Lawal ya kuma nanata muhimmancin azumin 'Sitta Shawwal' wato guda shi da ake yi a watan Shawwal.
Shin ko azumin Sitta Shawwal Bidi'a ne?
"Duk wanda ka ji yana cewa azumin Sitta Shawwal bidi'a ne to ko dai bai sani ba ko kuma akwai wani abu a zuciyarsa", in ji Sheikh Lawal Abubakar.