Yau ce ranar ƙarshe ta fitar da Zakkatul Fitr

Bayanan sautiLast Day of Zakkatul Fitr
An wallafa

Yau 1 ga watan Shawwal na shekarar 1442 wato ranar da al'ummar Musulmi a duniya ciki har da Najeriya da Ghana ke gudanar da Sallar Idi bayan kwashe kwanaki 30 suna azumin watan Ramadan.

Wani babban tsagi na ke cikasa ladan mai azumi shi ne zakkatul Fitr ko kuma Zakkar Fidda kai inda masu hali ke fitar da abinci su bai wa marasa shi domin samun zarafin abincin Sallah. Tundai daga ranar 27 ga watan Ramadan ake fara fitar da wannan zakka har zuwa kafin a fita sallar Idi.

Shin ko mene ne hukuncin wanda bai fitar da zakkar ba har aka je sallar Idi aka koma? Tabbayar kenan da Buhari Muhammad Fagge ya yi wa limamin masallacin Apo a Abuja, Sheikh Muhammad Nuruddeen wanda aka fi sani da Digital Imam.

Latsa hoton hatsi da ke sama domin sauraren hirar.