Abaya: Da gaske samari sun guji 'yan mata saboda kayan Sallah?
An wallafa
Muhawara ta kaure a shafukan zumunta na Arewacin Najeriya bisa zargin da wasu mata ke yi cewa samari sun guje su a watan Azumi domin ba sa so su kai musu kayan buda-baki ko na Sallah.
Sai dai samarin na cewa ayyukan ibada ne suka janye hankalinsu baya ga zafin aljihu da suke fama da shi.
Abokin aikinmu Abdulbai Jari ya bibiye wannan batu, ga karin bayaninsa: