Yadda za a kaucewa wa'azin da ke jawo rabuwar kai a Najeriya
An wallafa
Latsa hoton sama domin sauraren tattaunawar
Hukumomi a jihar Kaduna arewacin Njeriya sun gudanar da wani taro na malaman addinin Musulunci da nufin tattauna yadda za a kaucewa yin wa’azi da kan haifar da rarrabuwar kai tsakanin al’umma musamman yayin gudunar da tafsirin watan Ramadana.
Haka kuma taron ya duba yadda za a ci gaba da kiyaye matakan kariya daga cutar korona yayin fara gudanar da Tafsirin.
Yusuf Tijjani ya tattauna da Shiekh Hashim Bindawa babban limamin Masallacin Shiekh Dahiru Usman Bauchi da Shiekh Ishaq Al Madani babban limamin masallacin Matazu Road da ke Tudun Wada Kaduna da kuma Shiekh Jamil Al Bani Zaria Daraktan da ke kula da harakokin addinin musulunci a jihar Kaduna.