Gane mini Hanya: Matsalar ilimin ƴaƴa mata a jihar Kebbi
An wallafa
Latsa hoton sama domin sauraren rahoton Haruna Ibrahim Kakangi.
Ilimin ƴa mace wani abu ne da ke da matukar amfani a cikin al’umma, sai dai tsawon lokaci ƙarancin sanya yara makaranta ya kasance ɗaya daga cikin manyan matsaloli a Najeriya.
Wannan matsala ta fi Kamari ne a Arewacin kasar inda miliyoyin yara mata kan gaza samun ilimi sanadiyyar talauci ko kuma dalilai na ala’ada.
BBC ta ziyarci jihar Kebbi domin ganin yadda matsalar take.