Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Disina
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Bauchi Sheikh Dokta Ibrahim Disina ya ce sabanin fahimta da na aƙida ba sa hana shi mu'amala da kowane irin musulmai.
Dokta Disina ya ce tun da Allah bai hana shi mu'amala da wanda suke da saɓani a addini ba, to babu dalili da zai sa ya ƙi yin mu'amala da mabiyin dariƙun sufaye ko kuma wani da suke da saɓanin fahimta.
Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da BBC a cikin shirin Ku San Malamanku. Ya ce yana alaƙa da duk wanda alaƙa ta kama a yi da shi a cikin dukkan bangarori.
Sheikh Disina ya ce a cikin waɗanda yake hulɗa da su har da ƴan shi'a waɗanda suka taso tun suna yara, kuma har yanzu suna ci gaba da mu'amala.
Sai dai ya ce alaƙar ba ta sa ya ɓoye aƙidarsa ko fahitarsa a kan wani abu da addini.