Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus : Isra'ila ta soma yi wa Falasɗinawa riga-kafin cutar korona
Ƙasar Isra'ila ta fara yi wa dubban Falasdinawa allurar riga-kafin cutar korona.
Wadanda ke da lasisin aiki na Isra'ila za su karbi allurar riga-kafin Moderna a wuraren tsallakawa zuwa Babar Yammacin Kogin Jordan, da kuma a matsugunan Yahudawa.
Masu rajin kare hakkin dan adam sun yi kira ga Isra'ila ta kara himma sosai, suna masu cewa nauyin yi wa Falaɗinawa riga-kafin ya rataya ne a wuyanta.
A ƙalla Falasdinawa miliyan uku ba su samu riga-kafi ba a Gabar Yammacin Kogin Jordan, inda yawan masu kamuwa da cutar ke karuwa.
Ita dai Isra'ila ta musanta cewa ita ke da alhakin yi wa Falasiɗawan riga-kafi.
Yanzu haka ta yi wa fye da rabin ƴan kasarta allurar, kuma tuni tattalin arzikinta ya soma farfadowa.