Ƙayatattun hotunan Afirka a wannan makon: 5 zuwa 11 ga Fabrairun 2021

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotunan wannan makon daga nahiyr Afrika ko na ƴan Afirkar a wasu wuraren na duniya:

Mayar Sherif stares intently at the ball as she hits a return.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mayar Sherif ta kafa tarihi a ranar Talata a Gasar Australian Open inda ta zamo mace ƴar Masar ta farko da ta yi nasarar a gasar tennis ta Grand Slam. A nan kuma kwana biyu bayan hakan, sai Kaja Juvan ta Slovenia ta yi nasara a kanta.
Getnet Wale, Lamecha Girma and Selemon Barega of Ethiopia run in file.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata a Faransa, ɗan Habasha masu wasan tseren mita 3000 Lamecha Girma da Getnet Wale da kuma Selemon Barega sun fafata a wasan ƙarshe na Gasar Tsere Ta Duniya, inda Getnet ya yi nasara.
1px transparent line
1px transparent line
Primary school students wear masks and uniforms as they wait in a courtyard before lessons begin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Washegarin ranar a Luanda babban birnin ƙasar Angola, ɗalibai ne suka koma makaranta tun bayan rufe makarantu wata 11 da suka gabata, don daƙile yaɗuwar cutar korona.
A man feeds his dog with desert locusts that have invaded their farms during the second-wave invasion.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani manoma a Kenya na bai wa karensa farin ɗango yana ci a ranar Asabar da ta gabata. Farin ɗangon dai sun zama annoba da suka addabi manoma a gabashin Afirka.
A clerk shows two new Egyptian coins.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Lahadi aka ƙaddamar da sabbin sulalla a Masar, waɗanda aka yi don girmama ma'aikatan lafiya da ke ƙoƙarin daƙile annobar cutar korona.
Choir members sing during the Sunday mass without wearing masks and social distancing at Ufunuo na Uzima Church.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wannan ranar a Tanzaniya a wani coci da ke birnin Dar es Salaam, an ga yadda masu ibada ke waƙe-waƙe, sai dai babu bayar da tazara kuma ba sa sanye da takunkumi. Shugaban ƙasar ne ya ayyana ta a matsayin wacce ba ta fama da annobar cutar korona, duk da cewa kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen ƙasar.
A member of security forces takes part in a training session arranged by a security company in Tajoura suburb of Tripoli.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Laraba kuwa a Tripolic babbanbirnin Libiya, dakarun tsaro ne ke atisaye.
A woman walks with children towards the Meroe Pyramids. Nearby a man rides a camel.

Asalin hoton, Anadolu Agency/Getty Images

Bayanan hoto, Masu ziyara na tafiya wajen Dalar Meroe a kudancin Sudan ranar Juma'a.
A man riding his bike in Ziguinchor looks into the camera.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata, wani mutum kenan yana tuƙa kekensa a yankin Casamance da ke kudancin Senegal.
The port city of Oran covered in orange haze from a sandstorm.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a ƙurar hamada ta lulluɓe birnin Oran da ke gaɓar teku a Aljeriya, har launin wajen ya zama ruwan goron.

Dukkan hotunansuna da haƙƙn mallaka.