Boko Haram: Abin da muka sani game da harin dan aka kai Geidam

'Yan Bindiga

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Hukumomi a jihar Yobe sun yi karin haske game da harin da mayaƙan Boko Haran suka kai a garin Geidam a daren jiya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim, ya yi wa BBC karin bayani cewa sabanin yadda aka saba ganinsu a bayan gari, wannan karon mayakan na Boko Haram kafin su fara kai harin cikin garin na Geidam, sai da suka fara kai farmaki a ƙauyukan da ke kusa.

Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC yadda suka ji game da farmakin da maharan suka kai musu.

''Jiya daf da Sallar Magariba suka shigo mana cikin garin, ba su fita ba sai wajen tsakiyar dare, sun balle shagunan waya da na abinci suka kwashi kaya, shaguna uku dai na sani, kana sun ƙona motar wani mutum mai kirar Toyota Corolla a bakin kasuwa,'' in ji mazaunin garin.

Amma kuma in ji shi ya samu labarin cewa sun tafi da wasu jami'an kwastam uku, duk da cewa bai tabbatar ba.

Ya kuma ce sun riƙa jin ƙarar harbe-harbe, yayin da daga bisani wani jirgi mai sauƙar ungulu ya shigo yana ta shawagi a cikin garin.

Amma kuma ya bayyana cewa mutanen garin na ta mayar da martanin cewa kamar jami'an tsaron ba sa daukar matakan da suka kamata, ganin cewa a kwanakin baya ma sai da mayakan suka shigo cikin garin suka rika cin karensu ba babbaka.

Sai dai kuma ya ce, yanzu haka jami'an tsaron na nan na ta sintiri a cikin garin na Geidam.

Daya wani mazaunin garin shi ma ya shaida wa BBC cewa lokacin ana sallar Magariba suka shigo babu zato.

''Muna jin harbe-harben sai muka yi sauri muka shiga gidajenmu muka rufe, amma kuma mun samu labarin sun tafi da wasu jami'an kwastan uku,'' ya ce.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Yoben ASP Dungus Abdulkarim ya yi wa BBC karin bayani game da yadda mayakan suka shiga garin da cewa:

''Mun samu bayanan cewa sun bi wadannan kauyuka suka kwace wayoyin mutane, saboda kada su yi saurin kai labarin ɓullarsu zuwa cikin gari, don haka sun yi wa garin na Geidam ba-zata inda suka rika harbe-harbe ta ko ina a cikin daren.''

ASP Dungus ya kuma kara da cewa mayakan sun kai hari kan wasu shagunan ba bai bayyana yawansu ba, da suka hada da na sayar da kayan abinci, da na wayoyin salula da kuma na sayar da magunguna, inda suka kwashi kadadorin mutane.

Amma kuma ya ce daga bisani sojoji sun shigo suka yi artabu da su, inda suka fatattake su.

''Babu labarin asarar rayuka ko jikkata da muka samu kawo yanzu, amma me yiwuwa nan gaba za a iya samun ƙarin wasu bayanai game da harin,'' in ji Dungus.

Shin da gaske sun tafi da wasu jami'an kwastam?

army

Asalin hoton, Army

Bayanan hoto, A makon da ya gabata sojojin Najeriya suka kai hari wata babbar maboyar Boko Hram a dajin Timbuktu

ASP Dungus Abdulkareem ya shaida wa BBC cewa, duk da cewa an bayar da labarin cewa mayakan na Boko Haram sun yi awon gaba da wasu jami'an kwastam uku a yayin harin, amma kuma har yanzu ba su samu cikakken bayani game da tabbacin hakan ba.

Ya kuma ce ''a halin yanzu mutane sun fito sun ci gaba da harkokinsu, yayin da jami'an tsaro ke shawagi da sintiri don ƙoƙarin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a garin''.

Wasu rahotanni dai na cewa mayakan kan lallabo daga sabbin sansanoninsu da suka kafa a kauyukan Malari Zango da Abduri da Buhari da Degaltura da Kayidiri da Garin Liman da Gumsari Gagala da kuma Gorrgo duka a karamar hukumar Yusufari, da ke kewaye da garin na Geidam inda suke kai hari.

Galibi kuma sun tilasta wa mazauna wadannan kauyuka tserewa cikin garin na Geidam don neman mafaka.

Mayakan Boko Haram na shan kai farmaki a garin na Geidam, duk kuwa da matakan da hukumomi ke dauka.

Ko a kwanakin baya ma sai da suka kai wani mummunan hari a cikin babban asibitin garin da kuma shagunan da ke bakin kasuwa, inda suka kwashi magunguna da kayan abinci masu tarin yawa, suka kuma yi awon gaba da wani hakimi.