Covid-19: Riga-kafin Novavax na karfin kashi 89% a gwajin Birtaniya

An wallafa

Sabon riga-kafin Novavax na da karfin kashi 89 cikin 100 bayan gwaje-gwajen da aka yi masu yawa a Birtaniya.

Allurar mai suna Novavax ta kasance t afarko irinta da ke da tasiri kan sabon nau'in kwayar cutar korona da aka gano a Birtaniya, kamar yadda editan BBC na kiwon lafiya Fergus Walsh ya sanar.

Firaministan Birtaniya ya yi murna da samun wannan abin da ya kira "labari mai dadin ji", kuma nan kusa hukumar da ke tantance sahihancin magunguna ta ƙasar za ta yi bincike kan riga-kafin.

Birtaniya tuni ta yi odar allurai miliyan 60 na riga-kafin, wanda za a haɗa shi a wata masana'anta da ke yankin Stockton-on-Tees.

An kuma sa ran fara raba alluran riga-kafin a watanni shida na karshen wannan shekarar, da zarar hukumar Medicines and Healthcare Products Regulatory Agency (MHRA) ta Birtaniya ta amince da sahihancinsa.

Nadhim Zahawi shi ne ministan da ke da alhakin samar da wannan riga-kafin, uma ya ce: "Ni da kaina an shigar da ni cikin gwaje-gwajen wannan riga-kafin, kuma na yi murnar ganin sakamako mai karfafa gwuiwa da ya fito. Ina son mika godiya ta ga dubban waɗanda suka shiga cikin shirin gwajin, waɗanda da ba din su ba, to da wannan aikin ma bai samu ba."